Zabura ta 1
Albarka ga wanda bai shiga * shawarar miyagu ba,
bai tsaya a taron masu zunubi ba, * bai kuma zauna a gun masu yin ba’a ba.
Sai dai yana jin daɗin karanta shari’ar Yahweh, * yana ta nazarinta dare da rana.
Yana kama da itacen * da ke a gefen ƙorama,
yakan ba da ’ya’ya a kan kari, * ganyayensa ba sa yin yaushi, * yakan yi nasara a dukan abin
da yake yi.
Miyagu ba haka suke ba, * su kamar yayi suke * wanda iska take kwashewa.
Mai sama kuwa ba zai tallafa ba * miyagu a wurin hukunci * ko kuwa masu zunubi wurin adilai.
Sai dai Yahweh yana lura da taron adalai, * amma taron miyagu zai hallaka.
Zabura ta 2
Don me al’ummai suke tayarwa, * suna ƙirga mayaƙansu?
Don me sarakunan duniya suke yin tawaye, * masu mulkinsu suna gama kai
na gāba da Yahweh, * da shafaffen sarkinsa?
Suna cewa “Bari mu kwance igiyarsu, * mu fice daga ƙarƙashinsu.”
Shi wanda ke zaune a sama yana dariya, * yana mai da su abin dariya.
Sannan yana korar manyansu da hushinsa, * da hasalarsa kuma yana razana su.
Ni ma an naɗa ni sarkinsa * a bisa Sihiyona, dutsensa tsattarka.
Bari in yi shelar umurnin * Ubangiji Yahweh, * ya ce da ni:
“Kai ɗana ne, * a yau ne na haife ka.
Ka roƙe ni, zan ba ka * al’ummai ka gada, * har bangon duniya za ka mallaka.
Za ka yi kiwonsu da sandan ƙarfe, * ka farfashe su kamar tukunyar magini.”
Yanzu, ku sarakuna, ku yi hankali, * ku gargaɗu, ku mahukunta!
Ku bauta wa Yahweh da tsoro, * ku yi rawar jiki, ku da aka ƙaddarawa zuwa kabari,
don kada ya yi hushi, taronku kuwa ya hallaka, * gama yakan yi
hushi da sauri.
Albarka ga duk * masu neman mafaka a wurinsa.
Zabura ta 3
Yahweh, magabtana sun ƙaru ƙwarai! * Da yawa ne masu tasam mani!
Barkatai ne su ke hararrata, suna cewa: * “Ai ba wani taimakon da Allah zai yi masa.”
Amma kai, Yahweh, maigidana ne iyakar raina, * Maɗaukakina ne kuma, mai tallafata.
In na kai kukana gaban Yahweh, * yakan amsa mani daga tsattsarkan dutsensa.
In na kwanta in yi barci, * nakan farka, domin Yahweh yana kiyaye ni.
Ya Ƙaƙƙarfa, bana jin tsoron kiban magabtana, * da ke kewaye ta kowane gefe, ya Mai Sama.
Ka yinƙuro mana, Yahweh, * ka kuɓutad da ni, ya Allahna!
Kai da kanka * ka bugi bakin magabtana, * ka kakkarya haƙoran miyagu.
Ya Yahweh, kai mai nasara ne! * Albarkarka ga jama’arka.
Zabura ta 4
Da na yi kira, ka amsa mani, * ya Allah mai nasarata.
Daga matsatsi ka buɗe mani hanya, * ka ji tausayina, ka saurari addu’ata.
Ya ku ’yan adan, yaushe ne * za ku dena zagin Maɗaukaki?
kun bauta ma abubuwan banza, * kuna shawara da allolin ƙarya?
Amma dai ku san cewa * Yahweh zai yi abubuwan mamaki don bawansa, * Yahweh zai saurara sa’ad da na kira shi.
Ku ji tsoro, kada ku ɗau zunubi, * ku binciki zukatanku, * ku kwanta, ku yi kuka.
Ku yanka dabbobin da suka hallata hadaya, * ku kuma dogara ga Yahweh.
Mutane da yawa suke cewa, * “Wa zai kawo mana ruwan sama?
Hasken fuskarka * ya guje mana, Yahweh!”
Sai dai ka sanya farinciki a cikin zuciyata, * yanzu sai hatsinsu da abinshan inabinsu su ƙaru.
Da kwanciyar rai a gaban fuskarsa * zan kwanta in yi barci,
domin kai kaɗai ne, Yahweh, * kake zaunad da ni a cikin aminci.
Zabura ta 5
Ka kasa kunne ga kalmomina, Yahweh, * ka ji maganata.
Ka saurari sautin kukana, * ya Sarkina, Allahna, * domin gare ka nake addu’a.
Da sassafe ka ji muryata, * da sassafe nake yin ƙara, * in kuma yi dakonka.
Allolin banza ne ke jin daɗin mugunta, * mugun mutun ma ba zai zo gunka ba.
Masu fariya * kada su tsaya a gaban idanunka.
Na ƙi dukkan masu mummunan aiki, * sai ka hallaka maƙaryata.
Mai gunki da mai tsafi, * duk Yahweh yana ƙinsu.
Amma ni, da yalwar ƙaunarka, * zan shiga gidanka.
Zan yi sujada zuwa ga tsattsarkan Haikalinka * tare da masu tsoronka.
Ka yi mani jagora zuwa aljanna, * nesa daga magabtana; * ka sa hanyarka ta yi mani saukin bi.
Ba abin da za a gaskanta daga bakinsu, * cikinsu kududdufi ne da ba zai cika ba.
Maƙogwaronsu na haɗiya kamar buɗaɗɗen kabari, * suna kisa da halshensu.
Ka hallaka su, ya Allah, * bari shirye-shiryensu su tadiye su.
Saboda ɗumbun laifuffukansu * ka jefad da su * domin sun yi maka tawaye.
Duk waɗanda suka fake gare ka su yi farinciki, * kullun su yi ta raira waƙar murna.
Kakan kiyaye masu ƙaunar sunanka,* domin su yi matuƙar murna da kai.
Gama kana yi wa mai gaskiya albarka, * Yahweh, * kamar garkuwa, soyayyarka ke kewaye shi.
Zabura ta 6
Yahweh, kada ka tsawata mani da hushinka, * kada kuma ka hore ni da zafin ranka.
Ka ji tausayina, Yahweh, * domin na bushe.
Ka warkad da ni, Yahweh, * domin ƙasusuwana sun rafke.
Raina ya wahala ƙwarai, * amma kai, Yahweh, yaushe za ka dube ni?
Ka dawo, Yahweh, ka kuɓutad da raina, * ka cece ni yadda ya dace da ƙaunarka.
Gama ba mai tunawa da kai a Mulkin Mutuwa. * Can a Lahira ma wa zai yi yabonka?
Na gaji da kuka, * kowane dare sai na jiƙa gadona, * ina cika tabarmana da hawaye.
Idanuna sun dishe da baƙinciki, * zuciyata ta karaya saboda baƙinciki.
Ku rabu da ni, masu mugun aiki, * domin Yahweh ya ji sautin kukana.
Yahweh yā ji roƙona, * Yahweh ya karɓi addu’ata.
Su kunyata, su ɗauki rawar jiki * dukan magabtana * su juya, su ji kunya a Mahallaka.
Zabura ta 7
Yahweh, Allahna, gare ka nake dogara, * ka cece ni daga dukan masu korata.
Ka kuɓutad da ni, kada wannan ya kacancana ni * kamar zaki * yana ƙarya wuyana, ba kuma mai ceto.
Yahweh, Allahna, in na yi cin mutunci, * in hannuna na da laifi,
in na ci amanar abokina, * ko na dame shi da tsegumi,
to, magabcina ya bi ni, ya kama ni, * ya tattake kayan cikina a ƙasa, * ya jefad da antata a caɓi.
Ka tashi, Yahweh, da hushinka, * ka tsai da wulakancin magabtana.
Ka falka, ya Allahna, * ka umurci
Ka tattaro dukan kabilan kewaye da kai, * ka shugabance su, ya Maɗ aukaki, * Yahweh, ka yi wa dukan mutane shari’a.
Ka hukunta ni gwargwadon aikina na gaskiya * da kirkina, ya Maɗaukaki.
Ka rama ta’addancin ’yan ta’adda, * ka kuma kāre mai gaskiya.
Mai binciken zukata da hankula, * shi ne Allah mai gaskiya.
Maigidana Allah Maɗakukaki ne, * yakan ceci masu zuciya tagari.
Allah alkali ne mai gaskiya, * yana tsai da zalunci a kullun.
Bari Mai Nasara ya sake * wasa takobinsa, * ya ɗana bakansa cikin shiri.
Bari ya shirya makamansa masu kisa,* ya kunna kibansa masu wuta.
Mugu yakan ɗauki cuta, * yakan yi ciki da fitina, * yakan haifi ruɗu.
Ramin da ya haƙa ya tadiye shi, * ya faɗa ramin da ya tona.
Muguntarsa ta koma kansa, * rikicinsa ya sauka ƙoƙwan kansa.
Na gode wa Yahweh yadda ya kamata, * ina waƙar yabon Yahweh Maɗaukaki.
Zabura ta 8
Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ɗaukaka ne * a dukan duniya.
Zan yi wa martabarka sujada, * wadda take bisa sama, * da bakin jarirai masu shan mama.
Ka gina mafaka don gidanka, * bayan ka bebanta magabtanka * da maƙiyanka da masu ramuwa.
Sa’ad da na dubi sammai, * aikin yatsunka,
da wata da taurari * waɗanda ka halitta:
Menene mutun, har da za ka tuna da shi, * ko ɗan adan, har da za ka kula da shi?
Duk da haka, ka yi shi ya gaza alloli kaɗan, * da daraja da girma ka naɗa shi.
Ka mai da shi sarkin ayyukan hannuwanka, * ka sanya kome a ƙalƙashin sawayensa:
tumaki tare da shanu, * har da namomin jeji,
da tsuntsaye da kifayen teku, * masu yawo a hanyoyin ruwan tekuna.
Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ɗaukaka ne * a dukan duniya.
Zabura ta 9-10
Zan yabe ka, Yahweh, da dukan zuciyata, * zan bayyana dukan ayyukanka masu banmamaki.
Zan yi murna, in yi farinciki da kai, * zan raira waƙar da sunanka, Maɗaukaki.
Sa’ad da magabtana suke ja da baya, * suna tuntuɓe, su hallaka saboda hushinka.
Ka yi na’am da hakkina da sha’anina, * ka zauna a kan gadon sarauta, ya Alkalin gaskiya.
Ka tsawata wa al’ummai, ka hallaka miyagu, * ka shafe sunansu har abada abadin.
Magabtana su isa ƙarshensu, * su zama kufai har abada.
Ka tuge allolinsu masu tsare su, * a dena tunawa da su.
Ga shi, tun fil’azal Yahweh ya yi mulki, * ya kafa kursiyinsa don yin shari’a.
Shi ne yake mulkin duniya da gaskiya, * yana yi wa mutane shari’a da adalci.
Yahweh mafaka ne ga waɗanda ake zalunta, * matsera kuma a lokacin ƙunci.
Bari waɗanda suke son sunanka su amince da kai, * domin ba ka ƙyale masu nemanka, Yahweh.
Ku yi waƙoƙin yabon Yahweh, Sarkin Sihiyona, * ku gaya wa al’ummai aiyyukansa.
Gama yakan lura da masu kuka, * yakan tuna da nishinsu, * baya mantawa da ƙarar masu shan wuya.
Ka ji tausayina, Yahweh, * ka ga wahalata.
Ka janye ni daga Maƙiyina, * da ƙofofin Mutuwa,
don in bayyana yabonka sosai * daga ƙofofin ’Ya Sihiyona,
in yi farinciki * da nasararka.
Bari al’ummai su dulmuya cikin ramin da suka yi, * da tarkon da suka ɗana ya kama ƙafafunsu.
Bari Yahweh ya sanu ta hukuncin da yake zartaswa, * amma bari a kama mugu ta aikin hannuwansa.
Miyagu su koma Shawol, * su hallaka, su al’umman da suka manta da Allah.
Gama ba kullun ne za a manta da mabukata ba, * sazuciyar zaluntattu ma ba za ta dannu ba har abada.
Ka tashi, Yahweh, kada mutane su yi kirari, * a yi wa al’ummai shari’a a gabanka.
Yahweh, ka danne bakinsu, * ka sa al’ummai su san su mutane ne kawai.
10 Yahweh, don me kake tsaye can nesa, * kana ɓoyewa a lokacin wahala?
Cikin mugu yana dafa wulakanci, * da aniya yake aikata dabarun da ya ƙuƙƙulla.
Mugu yana fahariya da marmarinsa, * mai ƙwacewa ma yana bauta wa kwaɗayinsa.
Mugu yakan rena Yahweh, cewa: * “Mai Sama ba zai aikata hushinsa ba.
Allah ba zai jirkita dabarunsa ba, * wadatata za ta jure har abada.”
Maɗaukaki, hukuntanka suna nesa da shi, * daga birnin zuciyarsa yana firjinsu da ba’a.
Yana cewa da kansa, “Ba zan yi tuntuɓe ba, * ina da madauwamin farinciki ba wahala.
Bakinsa cike yake da zagi, zamba da zalunci, * halshensa yana riƙon wulakanci da mugunta.
Yakan yi kwanton ɓauna a ƙauyuka, * a maɓoya yakan kashe marasa aibu, * idanunsa na hararar kāsasse.
Yakan yi sanɗa kamar zaki a kogonnsa, * yakan yi sanɗa don ya kama gajiyayye, * yakan kama shi, ya tafi da shi.
A tarkonsa zaluntacce ke fāɗuwa, * marasa katari kuma na fāɗawa raminsa.
Yana cewa da kansa, “Allah ya mance, * ya rufe idonsa, * baya dubawa har abada.”
Ka tashi, Yahweh Allah, ka ɗaga hannunka, * kada ka manta da masu shan wahala.
Har abada ne mugu zai rena Allah? * yana cewa da kansa, “Ba zai yi hisabi ba.”
Ka dubi bakincikin da kanka, * ka dubi ɓacin ran, * gama hannunka ne ke bayas da su.
A gare ka gajiyayyen maraya ke danƙa kansa, * ka zama mataimakinsa mana!
Ka karya dantsen mugu, * ka biya shi da muguntarsa. * Ba ka ganin ƙetarsa?
Yahweh madauwamin sarki ne, * bari al’ummai su hallaka daga ƙasarsa.
Yahweh, ka saurari kukan matalauta, * ka mai da hankali, ka kasa kunne.
In ka kāre maraya da zaluntacce, * masu girman kai ba za su riƙa razana mutane daga duniya ba.
Zabura ta 11
Na sami mafaka wurin Yahweh. * Don me kuke sanɗar raina? * kuna farautata kamar tsuntsu?
Ga yadda miyagu suke jan baka, * suna ɗana kibansu,
don su harbi * masu gaskiya a ɓuye.
Lokacin da ake ture harsashen, * me Mai-Gaskiya yake yi?
Yahweh yana da mazauni a Haikalin, * kursiyin Yahweh a sama yake.
Idanunsa suna kallo, * suna binciken * duk ’yan adan.
Yahweh mai gaskiya * yana auna miyagu.
Duk wanda yake son zalunci * yana ƙin ransa.
Bari Yahweh ya zubo wa miyagu * garwashin wuta da kibiritu.
Bari iska mai ƙuna * ta zama rabonsu.
Yahweh mai gaskiya ne * yana son ayyukan gaskiya. * Fuska da fuska zamu kalli Mai-Kirki.
Zabura ta 12
Ka yi taimako, Yahweh, * domin masu ibada sun ƙare.
Amintattun mutane sun kasa * a cikin ’yan adan.
Kowa na zancen ƙarya, * da maƙwabcinsa.
Da baki mai lahani * da zuciya biyu suke magana.
Bari Yahweh ya yanka * duk baki mai lahani, * da duk halshe mai murɗa gaskiya,
waɗanda suke fariya cewa, * “Halshenmu shi ne ikonmu.
Makamanmu leɓunanmu ne, * wa zai mallake mu?”
“Saboda ajiyar zucin gajiyayyu * da nishin masu bukata,
yanzu zan tashi,” * in ji Yahweh.
“Zan ba da taimako * ga wanda ya ke bukatarsa.”
Alkawalan Yahweh * alkawalai ne masu gaskiya,
azurfa ne da aka tace a matoya, * aka tsabtace ta daga laka sau bakwai.
Yahweh, kai kā tsare mu, * kā kiyaye mu tun fil’azal, ya Madauwami.
Ko’ina miyagu suna rangadi, * suna tona ramuka don ’yan adan.
Zabura ta 13
Har zuwa yaushe za ka mance da ni, Yahweh? Har abada? * Har zuwa yaushe za ka kau da fuskarka daga wajena?
Har zuwa yaushe zan yi shakka a raina, * ina baƙinciki a raina? * Har zuwa yaushe maƙiyina zai yi mani dariya?
Ka dube ni, ka amsa mani, * Yahweh Allahna.
Ka buɗe mani idona, * ka kau da barcin mutuwa daga wajena.
Kada magabcina ya ce, * “Na rinjaye shi,” * kada maƙiyina ya yi farinciki saboda faɗuwata.
Amma ina dogara ga rahamarka, * bari zuciyata ta yi murna don ka cece ni.
Zan raira waƙa ga Yahweh, * gama Maɗaukaki ya kyautata mani.
Zabura ta 14
A tunanin wawayesuna cewa, * “Allah baya nan.”
Su ɓatattu ne, suna aikata al’amuran ƙyama, * ba wani mai yin abu mai kyau.
Daga sama Yahweh yana dubo * ’yan adan duka,
don ya ga ko akwai masu fahimi, * masu neman Allah.
Amma dukansu masu taurin kai ne, * sun ƙazanta gaba ɗaya.
Ba mai yin kyakkyawan aiki, * babu ko ɗaya.
Masu aikin mugunta ba su sani ba * cewa masu washe jama’arsa
suna satar hatsin Yahweh, * da ba su yi noma ba?
Ga yadda suka yi ƙungiya, * amma Allah ne a cikin jama’ar adilai.
Majalisar gajiyayyu ta kunyata miyagu, * gama Yahweh shi ne mafakarsu.
Daga Sihiyona sai ceton Isra’ila ya fito! * Sa’ad da Yahweh ya sake arzuta jama’arsa,
bari ’ya’yan Yakubu su yi farinciki, * ’ya’yan Isra’ila su yi murna.
Zabura ta 15
Yahweh, wa zai iya baƙunci a alfarwarka? * Wa zai iya zama a kan tsarttsarkan dutsenka?
Sai wanda ke bin hanya mara aibu, * yana aikata gaskiya, * yana faɗar kaskiya daga zuciyarsa,
Wanda baya kusƙure da halshensa, * baya cutar makwabcinsa, * baya baza jita-jita a kan abokansa.
Yakan rena mai laifi, * amma yakan shirya liyafa don masu tsoron Yahweh.
Ya rantse ba zai yi mugunta ba, * ba kuma zai canza ba.
Baya bayas da rance da ruwa, * baya ma karɓar toshi daga mayunwata.
Wanda yake yin waɗannan abubuwa * ba zai gaza ba.
Zabura ta 16
Ka kiyaye ni, ya Allah, * gama a gunka nike neman mafaka.
Na ce: “Yahweh, kai ne Ubangijina, * kai ne Nagartata, * ba wanda ya fi ka a sama.
Game da tsarkakan iskokin gargajiya, * jarruman da na ji daɗinsu dā,
baru nakuɗarsu ta ƙaru, * su daɗe cikin tsanani.
Hannuwana ba zasu zuba masu hadaya ba, * bakina ma ba zai ambaci sunayensu ba.
Yahweh, kā ba ni rabona na abin sha mai daɗi, * kā yi kuri’ar ƙasata.
An auna mani kyakkyawar ƙasa, * Maɗaukaki ya zaɓi ganduna.
Zan yabi Yahweh mai ba ni shawara, * da dare yana gargaɗina a zuci.
Na zaɓi Yahweh shugabana har abada, * daga hannun damansa ba zan girgiza ba.
Don haka zuciyata ke farinciki, antata ma ke murna, * jikina na zaune a cikin aminci.
Gama ba za ka sa ni a Mahallaka ba, * ba za ka bar mai bauta maka ya ga Ramin ba.
Za ka nuna mani hanyar rai, * kana cika ni da farinciki a gabanka, * da murna a hannun damanka har abada.
Zabura ta 17
Yahweh, ka ji roƙona don hakkina, * ka saurari kukana.
Ka kasa kunne ga addu’ata, * ka hallakad da bakunan yauɗara.
Bari adalcina ya yi haske a gabanka, * idanunka su dubi gaskiyata.
Ka gwada zuciyata, * ka bincike ni da dare, * ka jarrabce ni da wuta:
Ba za ka sami tsafi a wurina ba, * ban yi batanci game da aikin hannuwanka ba.
Ga kalmomin bakinka * na riƙe amana.
Ƙafafuna sun bi ta hanya mai wuya * ba su ratse daga hanyoyinka ba.
Ina kiranka, * ka amsa mani, ya Allah.
Ka kasa kunne gare ni, * ka ji maganata.
Ka yi karo da masu saɓonka, ya Maceci, * rufe bakunan magabtanka.
Ka adana ni kamar ƙwayar ido, * ka ɓoye ni a inuwar fukafukanka
daga mugun da ke son yayyaga ni * daga magabtana da ke kewaye da ni.
Sun naɗi gara, * suna magana da izgilanci sosai.
Ƙafafuna suna kyarma, * da suka kewaye ni.
Sun sa ido su fyaɗa ni * Ƙasar Hallaka,
kamar zaki mai haɗamar kisan abincinsa, * kamar kuyakuyan zaki masu ɓuya a wurin fako.
Ka tashi, Yahweh, ka tsai da hushinsu, * ka kā da su, * ka cece ni daga miyagun da ke yaƙinka.
Ka kashe su da hannunka, Yahweh, * ka hallaka su daga duniya, * ka shafe su daga masu rai.
Amma darajantattun mutanenka, * ka cika cikinsu da gara.
’Ya’yansu su sami duk abin da suke so, * su bar wadatarsu ga jikokinsu.
A ranar shari’a zan ga fuskarka. * a ranar tashin kiyama zan gamsu da zatinka.
Zabura ta 18
Ina ƙaunarka, Yahweh, ƙarfina. * Yahweh dutsena ne da matserata. * Allahna mafakata ne,
Tuduna ne kuma wurin da ni ke gudu, * da garkuwata da makamin ceto, * hasumiyata mai cancantar yabo.
Na yi kira ga Yahweh, * ya cece ni daga magabtana.
Raƙuman ruwan Mutuwa sun kewaye ni, * rafukan Hallaka sun gangara ta kaina.
Igiyoyin Mahallaka sun ɗaure ni, * tarkunan Mutuwa sun fuskance ni.
A shan wahalata na yi kuka ga Yahweh, * ga Allahna na yi kira don taimako.
Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata, * kukana ya kai har kunnuwansa.
Ƙarƙashin Ƙasa ya yi tangaɗi, * gindin duwatsu ma ya motsa, * ya yi makyarkyata da Yahweh ya fusata.
Hayaƙi ya fito daga hancinsa, * wutar gobara daga bakinsa, * har da garwashin wuta daga wajensa.
Ya buɗe sama, ya sauko, * girgijen hadari alfarwarsa ya ke.
Ya hau Kerub, ya tashi sama, * ya yi tafiya da fikafikai buɗe.
Tantinsa ya duhunta, * alfarwarsa da gajimaren ruwa.
Saboda haskensa gizagizai sun dāre a gabansa, * duk da kanƙara da harsunan wuta.
Yahweh ya yi tsawa daga sama, * Mafi ɗaukaka ya furta maganarsa.
Ya ƙera kibansa, ya warwatsa su, * ya yawaita walƙiyoyinsa, ya fatattake su.
Ƙalƙashin teku ya bayyana, * harsasan duniya sun tonu,
saboda tsautawarka, Yahweh, * saboda rurin hancinka.
Ya miƙo hannu daga sama ya ɗauke ni, * ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.
Ya kuɓutar da ni daga ƙaƙƙarfan Magabcina, * daga Maƙiyina da ya fi ni ƙarfi.
Ya bi da ni ranar mutuwata, * Yahweh ya zama sandata.
Ya fisshe ni daga Ƙasar Hallaka, * ya cece ni, domin ya ji daɗina.
Yahweh ya biya ni saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba ya saka mani da alheri.
Gama na kiyaye hanyoyin Yahweh, * ba ni da laifi, ya Allahna.
Gama dukan hukuncinsa na gabana, * ban kuwa yas da dokokinsa ba.
Kullun ina da sahihanci a gare shi, * na yi la’akari kada in yi masa laifi.
Don haka ya saka mani saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba a gaban idanunsa.
Ga mai aminci kai mai aminci ne, * ga mai sahihanci kai mai sahihanci ne.
Ga mai gaskiya kai mai gaskiya ne, * amma ga mai wayo kai ne mafi wayo.
Ai, kai ne Mai iko duka, * kana ceton gajiyayyu, * amma kakan tanƙwaso masu alfarma.
Kana yi mani haske, * fitilata Yahweh ne, * Allahna yana haskaka dufuna.
Ta wurinka ina da gwanintar sere, * da ikon Allahna na iya tsallace duk wani shinge.
Sarautar Allah kammalalliya ce, * ana tabbatad da umurninsa.
Shi shugaba ne * na duk masu dogara gare shi.
Gama wanene Allah in ba Yahweh ba? * Wanene kuma dutse in ban da Allahnmu?
Shi Allah ne da ke yi mani ɗamara da ƙarƙo, * da kuma Mai Bayarwa wanda sarautarsa take cikakka.
Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa, * ya sa in tsaya a kan tudunsa.
Ya hori hannuwana don yaƙi, * ya saukar mani da baka mai banmamaki.
Kā ba ni garkuwarka ta nasara, * da hannunka na dama kā riƙe ni, * da hoɓɓasanka na zama mai girma.
Kā ba ni dogayen ƙafafuna masu sauri, * idanun ƙafata ma ba su goce ba.
Na bi magabtana har na kama su, * ban juya baya ba sai da aka gama da su.
Na kā da su, ba su iya tashi ba, * sun fāɗi a ƙafafuna.
Kā yi mani ɗamara da ƙarfi don yaƙi, * kā kā da masu yaƙi da ni a ƙarƙashina.
Kā ba ni wuyan magabtana, * na hallaka maƙiyana.
Sun yi kuka, amma Macecin baya nan, * sun kira Yahweh Maɗaukaki, * amma bai amsa masu ba.
Na marmashe su sun zama kamar ƙurar titi, * kamar taɓon kwararo na tattake su.
Kā kuɓutad da ni daga kiban mutane, * kā tsare ni daga dafin sauran al’ummai.
Baƙuwar al’umma za ta zama baiwata, * da sun ji ni, nan da nan sai su yi mani biyayya, * baƙi sai sun sunkuya don tsoro.
Baƙi sukan yi rawar jiki, * zukatansu sukan karaya.
Ran Yahweh ya daɗe! * Dutsena a yabe shi! * Ɗaukaka ga Allah mai ba ni nasara!
Shi Allah ne wanda ya ba ni nasara, * ya sarayar da al’ummai gare ni.
Ya kuɓutad da ni daga Magabcina, * ya ɗaukaka ni a kan masu yin yaƙi da ni, * ya cece ni daga masu cin mutuncina.
Ya Maɗaukakin Zati, zan yabe ka a cikin al-ummai, * Yahweh, in kuma yi waƙar yabon sunanka.
Ya mai da sarkinsa sananne don cin nasara da ya yi, * ya nuna ƙauna ga shafaffen sarkinsa, * ga Dauda da irinsa har abada.
Zabura ta 19
Sammai suna shaida ɗaukakar Allah, * aikin hannuwansa ma, sararin sama ke bayyana shi.
Kowace rana tana furta magana ga rana ta biye, * kowane dare yana sanad da dare na biye.
Ba wata magana, ba wasu kalmomi, * ba a jin muryarsu.
A duniya duka kiransu ke bazuwa, * maganarsu kuwa har zuwa bangon duniya.
Ya kafa wa rana alfarwa, * kamar ango tana taƙama daga maɓoyarta.
Tana murna kamar mayaƙi, * don ta ruga a kan hanyarta.
Takan fara daga farkon sama, * ta koma gare shi, * ba ta kuskuren ɗakinta.
Shari’ar Yahweh kammalalliya ce, * tana sanyaya zuciyata.
Shari’ar Yahweh tabbatacciya ce, * tana sa hikima a tunanina.
Ka’idodin Yahweh madaidaita ne, * suna faranta zuciyata.
Umurnin Yahweh mai haske ne, * yana haskaka idanuna.
Dokar Yahweh mai tsabta ce, * tana jurewa har abada.
Hukuntan Yahweh gaskiya ne, * dukansu daidai ne.
Su aka fi so a kan zinariya, * komi yawanta.
Sun fi zuma zaƙi, * i, fiye da saƙa cike da ruwan zuma.
Suna haskaka ni bawanka, * wajen kiyaye su da lada mai girma.
Wa zai iya gano kurakurai? * Ka hana ni bauɗewa.
Ka kuma kare ni daga allolin ƙarya, * kada su mallake ni.
A sa’an nan ne zan zama kamili, * in kuma kuɓuta daga babban zunubi.
Sai bakina ya furta abin da ya gamshe ka, * zuciyata ma ta bi nufinka, * Yahweh, Dutsena da Mai Fansata!
Zabura ta 20
Yahweh ya ba ka nasara a ranar wahala! * Sunan Allah na Yakubu ya zama garunka.
Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa, * ya kawo maka gudunmuwa daga Sihiyona.
Ya tuna da dukan baye-bayenka, * ya yi na’am da hadayunka na ƙonawa.
Ya biya bukatar zuciyarka, * ya cika dukan shirye-shiryenka.
Sannan za mu yi sowa ta farinciki saboda ka ci nasara, * da sunan Allahnmu kuma za mu kaɗa tutoci. * Bari Yahweh ya cika dukan roƙe-roƙenka!
Yanzu dai na sani * Yahweh yakan ba shafaffen sarkinsa nasara.
Yakan ba shi nasara daga tsattsarkar samaniyarsa, * a mafakarsa yakan ba da nasara da
hannunsa na dama.
Waɗansu suna da karusai, * waɗansu suna da dawaki,
amma mu da sunan Yahweh * Allahnmu ne muke da ƙarfi.
Suna sunkuyawa, suna faɗi, * amma mu, muna tashi tsaye kyam.
Yahweh yā ba sarkin nasara, * yā ba shi nasara da muka roƙa.
Zabura ta 21
Yahweh, da nasararka sarki yake murna, * da agajinka yake farinciki.
Kā biya masa burin zuciyarsa, * ba ka ƙyale roƙon da ya yi ba.
Kā zo gare shi da albarka mai kyau, * kā sanya kambin zinariya a kansa.
Ya roƙe ka madauwamin rai, ka kuma ba shi, * kwanaki ba iyaka, har abada abadin.
Martabarsa babba ce don nasarar da ka ba shi, * kā sa ya yi suna da kwarjini.
Albarkarka tana a kansa har abada, * za ka faranta masa rai da ganin fuskarka.
Sarkin yana dogara ga Yahweh, * ba kuma zai kawu daga ƙaunar Madaukaki ba.
Hannunka na hagu ya kama dukan magabtanka, * hannunka na dama ya kama maƙiyanka.
Yahweh, kā sa su a cikin tanderu mai wuta * a lokacin hushinka.
Da hushinsa yā cinye su da wuta, * ya haɗiye su.
Kā hallaka ’ya’yansu daga duniya, * da zuriyarsu daga cikin ’yan adan.
Gama sun shirya tayarwa game da kai, * sun ƙulla mugunyar dabara, * amma ba su iya yinta ba.
Kā sa su durkusa, * inda kake ɗana masu bakanka.
Yahweh, ka yi bikin nasararka! * Za mu raira waƙa ta yabon ikonka.
Zabura ta 22
Ya Allahna, ya Allahna, * don me ka yashe ni?
kana korar roƙona, * da sautin kururuwata.
Ya Allahna, ina kira da rana, * amma ba ka amsa ba,
da dare kuma, * ban sami ta’aziya ba.
Amma kana zaune a kan tsattsarkan gado, * Ɗaukakar Isra’ila.
Gare ka ne kakanninmu suka dogara, * sun dogara, kai ma ka kuɓutad da su.
Gare ka ne suka yi kira, sun kuwa kuɓuta, * gare ka ne suka yi kira, ba su kuwa kunyata ba.
Amma ni tsutsa ne, ba mutun ba, * mafi renanne wurin mutane, * abin ba’a ga kowa.
Duk waɗanda ke ganina suna maishe ni abin dariya, * suna tsaki, suna kaɗa kai, suna cewa:
“Ya bi Yahweh, bari ya kuɓutad da shi; * sai ya cece shi in ya so shi.”
Amma kai ne ka fito da ni daga mahaifa, * ka kwantad da raina a maman mahaifiyata.
Kai ne ka ciyad da ni daga haifuwata, * tun ina cikin uwata kai Allahna ne.
Kada ka yi nesa da ni, * gama masu tsananta sun yi kusa, * ba ma wani mataimaki.
Bajimai masu yawa suna kewaye ni, * ƙarfafan bajimai daga Bashan suna sa ni tsaka.
Suna buɗe mani bakinsu, * kamar zakoki masu kāwa masu hauka.
An zub da ni kamar ruwa, * ƙasusuwana duka sun guggulle.
Zuciyata ta narke kamar danko * tana ɗigowa daga ƙirjina.
Ƙarfina ya bushe kamar sakaina, * halshena ya liƙe wa muƙamuƙaina, *
an tura ni cikin caɓin Mutuwa.
Gama karnuka sun kewaye ni, * ƙungiyar miyagu ta sa ni a tsaka,
sun cinye naman hannuwana da ƙafafuna. * Na iya ƙirga dukan ƙasusuwana.
Ga yadda suke kallona, suke zura mani ido, *
suna rarraba tufafina a junansu, * rigata kuwa suna ƙuri’a a kanta.
Amma kai, Yahweh, kada ka yi nisa, * ya Rundunata, ka gaggauta ka taimake ni!
Ka ceci wūyana daga takobi, * da fuskata daga ruwan gatari.
Ka kuɓutad da ni daga bakin zaki, * ka sa in rinjayi ƙahonin ɓakwane,
don in yi shelar sunanka ga ’yan’uwana, * in yabe ka a tsakiyar jama’a.
Masu tsoron Yahweh, ku yaba masa, * ku jikokin Yakubu, ku girmama shi, * ku tsorace shi, dukan jikokin Isra’ila.
Gama bai rena ba, * ko ƙin waƙar gajiyayye.
Bai kuma kau da fuskarsa daga gareshi ba, * amma da ya yi kuka, yā ji shi.
Zan raira yabonka sau ɗari * wurin babbar jama’a * zan biya alkwaran da na rantse, ya Shugaba.
Masu tsoronsa za su ci abinci, * matalauta za su ƙoshi.
Masu neman Yahweh za su yaba masa, * zukatanku su daɗe har abada!
Dukan iyakokin duniya za su tuna, * su komo wa Yahweh.
Dukan kabilan al’ummai ma * za su yi maka sujada.
Gama Yahweh sarki ne, * mai mulki kuma na al’ummai.
Lalle, dukan masu yin barci a Lahira * za su yi masa sujada.
Duk waɗanda suka sauka a Caɓin * za su durƙusa masa, * gama Mai nasara yakan mayar da rai.
Bari jikokina su bauta masa, * su ba da labarinsa har abada.
Su soma ba da shaidar nagartarsa * ga mutanen da za a haifa, cewa ya yi abin.
Zabura ta 23
Yahweh makiyayina ne, * ba zan yi rashi ba, * zai sa ni in kwanta wurin ɗanyar ciyawa.
Zai bi da ni wurin ruwan de ke kwance, * don ya farfaɗo mani da rai.
Zai bishe ni wuri mai yawan ciyawa, * kamar yadda ya dace da sunansa.
Ko da yake ina tafiya * ta tsakar duhu baƙiƙ ƙirin,
ba zan ji tsoron hatsari ba, * domin kana tare da ni.
Sandarka da kerenka * ba shakka za su yi mani jagora.
Kakan shirya mani abinci * a gaban magabtana.
Kakan shafa mani mai a ka, * ƙoƙona ya cika har yana zuba.
Ashe, alheri da rahama za su raka ni * duk kwanakin raina.
Zan kuma zauna a gidan Yahweh * kwanaki marasa iyaka.
Zabura ta 24
Ƙasa da duk wadatarta na Yahweh ne, * da duniya da mazaunanta.
Gama ya gina ta a bisa tekunan da ke ƙarƙashin ƙasa, * ya kafa harsashinta bisa igiyar tekuna.
Wa zai hau kan dutsen Yahweh? * Wa zai tsaya a tsattsarkan wurinsa?
Sai wanda hannunsa da zuciyarsa ba su da aibu, * wanda bai juya nufinsa ga gunki ba, * ko kuma ya rantse a kan allahn ƙarya.
Shi ne zai karɓi albarka daga wurin Yahweh, * da nagarta daga Allahnsa maceci.
Ku nemi Sarkin zamanai, * ku bi Wanda ya zauna tare da Isiyaku.
Ku ɗaga kanku, ya ku ƙofofi, * ku ɗagu, ku ƙofofin Madauwami, * Sarkin ɗaukaka na zuwa.
Wanene Sarkin ɗaukaka? * Yahweh ne mai ƙarfi mai iko, * Yahweh mai iko a yaƙi.
Ku ɗaga kanku, ya ku ƙofofi, * ku ɗagu, ku ƙofofin Madauwami, * Sarkin ɗaukaka na zuwa.
Wanene Sarkin ɗaukaka? * Yahweh ne mai runduna, * shi ne Sarkin ɗaukaka.
Zabura ta 25
A gare ka, Yahweh, * ni ke sa raina.
Ya Allahna, a gare ka ni ke dogara, * kada in kunyata, * kada magabtana su yi murna a kaina.
Duk wanda ya kira ka ba zai kunyata ba, * sai matsegunta marasa aminci su kunyata.
Ka nuna mani hanyoyinka, Yahweh, * ka koya mani tafarkunka.
Ka sa in bi ka da aminci, ka ma koya mani, * domin kai ne Allah mai cetona, * gare ka ni ke kira duk yini.
Ka tuna, Yahweh, da rahamarka da alherinka, * yadda tun fil’azal suke.
Zunubaina da kurakuraina na ƙuruciyata, * kada ka tuna da su!
Amma ka tuna da ni bisa ga alherinka, * bisa ga ƙaunarka, Yahweh.
Yahweh mai nagarta da gaskiya ne, * Maɗaukakin Zati, ya kan koya wa masu zunubi hanyarsa.
Yakan bi da matalauta ta adalcinsa, * yakan koya masu hanyarsa.
Dukan hanyoyin Yahweh alheri ne da aminci * ga waɗanda suke kiyaye ka’idodin yarjejeniyarsa.
Albarkacin sunanka, Yahweh, * ka gafarta zunubina, * ko da yake babba ne.
Wane mutun ne ke tsoron Yahweh? * Shi ne wdanda zai koya wa hanyar da zai zaɓa.
Ransa zai zauna lafiya, * jikokinsa ma za su gaji ƙasar.
Zumuncin Yahweh ya ɗauru da masu tsoronsa, * yana sanar masu da yarjejeniyarsa.
Idanunna kullun ga Yahweh ne, * domin zai kau da ƙafafuna daga tarko.
Ka dube ni, ka ji tausayina, * domin ina kaɗaici a cikin matsatsi.
Damuwa ta matsa wa zuciyata, * ka fid da ni daga ɓacin raina.
Ka dubi wahalata da azabata, * ka kawas da dukan zunubaina.
Ka dubi yawan magabtana, * masu ha’inci da su ke ƙina.
Ka kiyaye raina, ka kuɓutad da ni, * kada in kunyata, domin na nemi kāriya a wurinka.
Ka sa nagarta da aminci su kiyaye ni, * domin na kire ka.
Ya Allah, ka ceci ’ya’yan Isra’ila * daga dukan wahalarsu.
Zabura ta 26
Ka hukunta ni, Yahweh, * gama na riƙa bin gaskiya.
Na dogara ga Yahweh, * ban girgiza ba.
Ka bincike ni, Yahweh, ka auna ni, * ka gwada zuciyata da tunanina.
Lalle, a kullun ƙaunarka tana cikin hankalina, * ina kuma bin ka da aminci.
Ban zauna da masu bautar gumaki ba, * ban shiga gidan masu jahilci ba.
Na tsargi taron masu aikata mugunta, * ban taɓa zama da miyagu ba.
Na wanke hannuwana ba tare da aibu ba, * don in zagaya bagadinka, Yahweh,
don in ɗaga muryar yabonka, * in faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
Yahweh, ina ƙaunar zama a gidanka, * inda ɗaukakarka take.
Kada ka runtume ni da masu zunubi, * ko haɗa raina da matsafa.
A hannunsu na hagu akwai gumaka, * hannunsu na dama cike ya ke da cin hanci.
Ni kam, zan riƙa yin halin kirki, * ka fanshe ni, ka yi mani rahama.
Ƙafata ta tsaya daram da masu gaskiya, * a cikin taronsu ne nike durƙusa wa Yahweh.
Zabura ta 27
Yahweh ne haskena da cetona, * to, wa zan ji tsoro?
Yahweh ne mafakar raina, * to, wa zai sa in firgita?
Sa’ad da miyagu suke yaƙina * don su ci namana,
maƙiyana da magabtana * suna tuntuɓe, suna fāɗuwa.
Ko da rundunar soja ta kewaye ni, * zuciyata ba za ta razana ba.
Ko da mayaƙa sun taso mani, * zan yi taho mu gama da su.
Abu guda na roƙa sau ɗari, * shi ne, Yahweh, ni ke nema:
In zauna a gidan Yahweh, * dukan kwanakin raina,
in ga kyan Yahweh, * in tashi kowace safiya a cikin Haikalinsa.
Zai darajanta ni a Zaurensa, * bayan Mugunyar Rana.
Zai ɓoye ni a innuwar tantinsa, * a kan dutse mai tsayi.
Yanzu an ɗaga kaina * bisa magabtana da ke kewaye da ni.
Zan yanka hadayun murna a tantinsa, * zan yi kiɗa da waƙa ga Yahweh.
Ka ji muryata, Yahweh, lokacin da na yi kira, * ka ji tausayina, ka amsa mani.
“Zo mana,” in ji zuciyata, “ka nemi fuskarsa!” * Fuskarka zan nema, Yahweh.
Kada ka juya mani baya, * kada ka watsar da bawanka cikin hushi, * ka zama mataimakina.
Kada ka ƙi ni, * kada kuwa ka yashe ni, * ya Allah mai cetona.
In ubana da uwata sun yashe ni, * Yahweh zai riƙe ni.
Yahweh, ka nuna mani hanyarka, * ka yi mani jagora a hanyarka mara gargada * saboda magabtana.
Kada ka bari magabtana su haɗiye ni, * don akwai shaidar zur a kaina, * suna magana da magudi.
Na amince da Mai Nasara, * don in ga kyan Yahweh * a ƙasar rai madauwami.
Ka jira Yahweh, ka ƙarfafa, * bari zuciyarka ta ɗaure * ka jira Yahweh.
Zabura ta 28
A gare ka, Yahweh, nike kira, * Dutsena, * kada ka ƙi amsa mani.
In ba ka amsa mani ba, * zan yi kama da waɗanda suka gangara Ramin.
Ka ji roƙona don jinƙai, * da nike kira gare ka,
da nike ɗaga hannuwana * wajen tsarkakken dandalinka.
Kada ka haɗa ni da miyagu, * ko masu aikata mugunta.
waɗanda ke maganar salama da maƙwabtansu, * amma zukatansu cike suke da ha’inci.
Ka yi masu abin da suka yi, * da sakayya gwargwadon ayyukan da suka yi.
Ka biya su bisa ga aikin hannuwansu, * ka ba su abin da ya cancance su.
Gama ba su kula * da abin da Yahweh ya yi ba, * ko kuwa aikin hannuwansa.
Shi ma zai rushe su, * ba kuwa zai sake gina su ba.
Yabo ga Yahweh! * domin ya ji roƙona na jinƙai.
Yahweh ne garkuwata mai ƙarfi, * zuciyata ta amince da shi.
Na koma ƙuruciyata, * zuciyata tana murna, * da waƙata zan yabe shi.
Yahweh makara da mafakarmu, * shi Macecin shafaffen sarkinsa ne.
Zabura ta 29
Ku biya wa Yahweh, ku alloli, * ku biya shi ɗaukaka da yabo, * ku biya Yahweh abin da ya dace da sunansa.
Ku rusuna a gaban Yahweh. * Mai-Tsarkin ya bayyana.
Ana jin muryar Yahweh a bisa tekuna, * Allah Maɗaukaki yana tsawa, * Yahweh yana ƙara bisa teku.
Muryar Yahweh ƙarfi ce, * muryar Yahweh ɗaukaka ce.
Muryar Yahweh na tsaga itatuwan al-ul, * Yahweh na tsaga itatuwan al’ul na Labanon.
Muryar Yahweh tana tatsatsi * da harsunan wuta.
Yana sa Labanan tsalle kamar ɗan maraƙi, * da Sirion kamar ɗan sa.
Muryar Yahweh tana girgiza ƙasar jeji, * tana girgiza ƙasar jejin Kadesh.
Muryar Yahweh tana sa bareyi haifuwa, * tana zabge ganyen daji duka,
a cikin Haikalinsa kuma * Maɗaukakin yana bayyana.
Tun ruwan tsufana Yahweh ya zauna gadon mulkinsa, * tun fil’azal Yahweh sarki ne.
Yahweh yakan ba jama’arsa nasara. * Yahweh yana sa masu albarka da salama.
Zabura ta 30
Ina girmama ka, Yahweh, * gama ka ta da ni, * ba ka kuma bar magabtana su yi mani dariya ba.
Yahweh Allahna, * na yi kuka gare ka, * ka ma warkad da ni.
Yahweh ya tsamo ni daga Shawol, * bayan gangarawata a Rami ka mayar mani da rai.
Ku yi waƙa ga Yahweh, ku masu bautarsa, * ku yabi sunansa mai tsarki.
Gama mutuwa tana cikin hushinsa, * amma rai madauwami yana wurin alherinsa.
Da duhu ya yi ana kwanciya da kuka, * amma da Asuba ana tashi da sowa ta murna.
A wautance sai na ce, * “Har abada ba zan yi tuntuɓe ba.”
Yahweh, alherinka ya ƙarfafa ni * fiye da manyan tsaunuka.
Amma da ka kau da fuskarka, * sai na jijjiga ƙwarai.
Ina kira gare ka, Yahweh, * Ubangijina, ina neman jinƙai.
Wane amfani za a samu daga hawayena? * ko gargarawata Ramin?
Caɓi zai taɓa yabonka? * ko zai yi shelar amincinka?
Yahweh, kasa kunne, ka ji tausayina, * Yahweh, ka zama mai taimakona.
Ka mai da makokina rawa, * ka kwance tsummokina, ka yi mani ɗamara da murna.
Bari zuciyata ta yi waƙar yabonka, * kada in sake yin bakinciki.
Yahweh Allahna, * zan gode maka har abada.
Zabura ta 31
A gare ka, Yahweh, na zo neman tsari, * kada in kunyata, ya Madauwami, * a cikin amincinka ka fanshe ni.
Ka kasa kunne gare ni, * ka cecei ni da hanzari.
Ya Dutsen mafaka, ka zama nawa, * ya Barikin Tsira, ka cece ni.
Gama kai ne dutsena wurin tsira, * albarkacin sunanka za ka yi mani jagora, ka nuna mani hanya.
Za ka ’yanta ni daga tarkon * da suka ɗana mani, * domin kai ne mafakata.
A cikin hannunka nike danƙa ruhuna, * ka fanshe ni, Yahweh Allah.
A gaskiya na ƙi * jinin masu bautar gumakan banza.
Na dogara ga Yahweh, * zan yi farinciki da murna saboda alherinka.
Lokacin da ka ga wahalata, * kā lura da ni gāba da Magabci.
Ba ka ƙulle ni a hannun Magabci ba, * ba ka ma sa ƙafafuna cikin Mugun Daji ba.
Yahweh, ka ji tausayina, * gama ina cikin shan wahala.
Idona ya lalace da baƙinciki, * har da maƙogwarona da cikina.
I, rayuwata ta gaji saboda makoki, * shekaruna kuma saboda nishi.
Ƙarfina ya gaza cikin wahala, * ƙasusuwana sun tabke, * ana kuma cin kayan cikina.
Na zama abin ba’a har ma ga maƙwabtana, * na zama bala’i mai ban tsoro ga abokaina; * waɗanda suka gan ni a hanya suna guduna.
Na yanƙwane, ba hankali kamar matacce, * na zama kamar fasasshen tulu.
Gama ina jin raɗe-raɗe masu yawa, * ta ko’ina razana ta kewaye ni,
lokacin da suka taru suna shawara a kaina, * suna ƙulla maƙircin kashe ni.
Amma a gare ka na dogara, * Yahweh, * ina cewa, kai ne Allahna.
Matakan rayuwata suna a hannunka, * ka cece ni daga hannun magabtana * da na masu matsa mani lamba.
Ka sa fuskarka ta haskaka bawanka, * ka cece ni ta alherinka.
Yahweh, kada in kunyata, * lokacin da nike kiranka.
Bari miyagu su kunyata, * a jefad da su Shawol.
Ka yi wa leɓunan maƙaryata takunkumi, * waɗanda ke maganar fariya da gaba gaɗi * ga Mai Gaskiya Mai Zamanu.
Abubuwan alherai barkatai ne * ka shirya wa waɗanda suke jin tsoronka,
abubuwan da ka tanada wa masu dogara gare ka, * a gaban mutane.
Kā ɓoye su a maɓoyar zatinka * daga ƙarairayin mutane.
Kā kare su a zaurenka * daga tankiyar harsuna.
Alhamdu ga Yahweh! * Gama ya nuna mani ƙauna mai bammamaki * daga ƙaƙƙarfan birninsa.
Dā fargabata tana sa in zaci: * “An raba ni a gabanka.”
Amma kā ji roƙona na jinƙai * lokacin da na yi kira gare ka.
Ku ƙaunaci Yahweh, dukanku masu bauta masa, * gama Yahweh yana kiyaye amintattunsa.
Amma yana sakayya mai zafi * ga masu aikata izgili.
Ku ƙarfafa zukatanku, * dukanku masu sa zuciya ga Yahweh.
Zabura ta 32
Albarka ga wanda aka yafe wa laifinsa, * wanda aka gafarta zunubinsa.
Albarka ga wanda Yahweh bai sa wa laifi ba, * wanda ba zamba a ransa.
Amma ni kamar fasassar tukunya nine, * ƙasusuwana sun rafke * saboda nishina wuni zubut.
Ya Maɗaukaki, dare da rana * hannunka yana yi mani nauyi.
Na kaɗu, ya Shaddai, * kamar farin bazara.
Na sanad da zunubina gare ka, * ban kuma ɓoye laifina ba.
Na ce, “Maɗaukaki, zan faɗi * laifofina, Yahweh.” * Kā gafarta kurena da zunubina.
Don haka ya kamata kowane mai bauta maka * ya yi addu’a zuwa gunka.
Lokacin da runduna ta kusato, * ko babbar ambaliyar ruwa ta malalo, * ba za su kai gare shi ba.
Kai ne mafakata, * ka kiyaye ni daga masu afka mani, * ya Matsarata, ka cece ni, ka kewaye ni.
Zan karantad da kai in koya maka * hanyar da za ka bi. * A kullun idona baya rufu gare ka.
Kada ka zama kamar doki * ko alfadari mara hankali.
Da ragama da linzami ne * za a iya sarrafa shi, * sannan ka kusance shi.
Azabun miyagu da yawa suke, * amma duk wanda ya dogara ga Yahweh, * da ƙauna zai rungume shi.
Ku yi farinciki da murna ga Yahweh, ku adilai, * ku yi sowar farinciki, dukanku masu zucya ta kirki.
Zabura ta 33
Ku yi farinciki ga Yahweh, ku masu gaskiya, * ku yabi Maɗaukaki, ku adalai.
Ku yabi Yahweh da molo, ku kaɗa masa garaya mai tsarkiya goma.
Ku raira masa sabuwar waƙa, * ku yi kiɗi da gwaninta da muryoyi masu daɗi.
Gama maganar Yahweh daidai ta ke, * dukan ayyukansa kuma abin dogara ne.
Yana ƙaunar abin da ke na adalci da adalci, * da alheri Yahweh ya cika duniya.
Da umurnin Yahweh aka yi sammai. * Ta kalmar da ya faɗi * aka yi rundunar taurari.
Yana tara tekuna a cikin tulu, * yana sa zurfafan tekuna a cikin rumbu.
Ku ji tsoron Yahweh, ku dukan duniya, * girmama shi ku dukan mazaunan duniya.
Ya yi magana, ta zauna, * ya yi umurni, abubuwan sun kasance.
Yahweh yana sukulkuce shirin al’ummai, * yana mai da tsare-tsaren jama’a banza.
Amma shirin Yahweh ya tabbata tun fil’azal, * manufofinsa ma na dukan zamanai ne.
Mai murna ce al’ummar * da Yahweh Allahnta ya albarkace ta,
jama’ar da ya zaɓa * ta zama abin gadonsa.
Yahweh yana kallo daga sama, * yana ganin dukan ’yan’adan.
Daga inda ya zauna a kan kursiyinsa yana kallon * dukan mazaunan duniya.
Mahallicin yana binciken zukatansu, * Mai-Gani yana kallon dukan ayyukansu.
Sarki baya nasara * da ƙarfin mayaƙa.
Haka ma jarumi baya kuɓuta * saboda ƙarfinsa.
Dokinsa baya da amfani don cin nasara, * haka ma ƙarfin rundunar yaƙinsa don kwana lafiya.
Yahweh yana kare masu tsoronsa, * waɗanda ke dogara ga alherinsa.
Yana cetonsu daga mutuwa, * daga yunwarta yake kare rayukansu.
Ga Yahweh muke sa zuciya, * Shi ne mai tsare mu da garkuwarmu.
Muna murna saboda shi, * mun amince da sunansa mai tsarki.
Yahweh, ka sa tausayinka ya kasance tare da mu, * tun da a gare ka muke sa zuciya.
Zabura ta 34
Zan albarkaci Yahweh kulluni, * a kowane lokaci yabonsa yana bakina.
A wurin Yahweh ruhuna zai sami ɗaukaka, * bari gajiyayyu su ji, su yi murna.
Ku taya ni girmama Yahweh, * mu ɗaukaka sunansa tare.
Na yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa mani, * daga dukan fargabana ya kuɓutad da ni.
Sun dube shi, fuskokinsu sun yi haske, * ba za su kunyata ba har abada.
Gajiyayyen nan ya yi kira, * Yahweh ya ji shi, * daga dukan ɓacin ransa ya cece shi.
Mala’ikan Yahweh yana sintiri * kewaye da masu tsoronsa, * domin ya cece su.
Ku ɗanɗana, ku tsotsa sosai, * gama Yahweh yana da zaƙi, * mai albarka ne mutumin da ya amince da shi.
Ku ji tsoron Yahweh, ku tsarkakansa, * gama masu jin tsoronsa ba za su rasa kome ba.
Mawadata za su yi talauci, su yi yunwa, * amma masu neman Yahweh, ba za su rasa albarka ba.
Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni, * zan koya maku tsoron Yahweh.
Akwai wani mutun da ke son tsawon rai? * da lokaci don ya daɗe yana cin albarka?
To, ka tsare halshenka daga mugunta, * leɓenka kuma maganganun ƙarya.
Ƙi mugunta, ka aikata alheri, * nemi salama, ka bi ta.
Idanun Yahweh suna kallon masu gaskiya, * kunnuwansa kuma suna sauraren kukansu.
Hushin Yahweh kan masu aikata mugunta ya ke, * domin ya shafe tunawa da su a duniya.
Lokacin da masu gaskiya suke yin kuka, Yahweh yana jinsu, * don ya cece su daga dukan ƙacin ransu.
Yahweh na kusa da waɗanda suka karai, * waɗanda suka fid da zuciya ma yana cetonsu.
Gwaje-gwajen masu gaskiya yawa gare su, * amma daga dukansu Yahweh yana cetonsu.
Yana lura da dukan ƙasusuwansa, * ko ɗayansu ba zai karye ba.
Ƙeta zata kashe mugu, * maƙiyan masu gaskiya ma za su hallaka.
Yahweh yana fansar rayukan bayinsa, * masu amince wa shi ma ba za su hallaka ba.
Zabura ta 35
Yahweh, ka yi faɗa da masu faɗa da ni, * ka yi yaƙi da masu yaƙi da ni.
Ka ɗauki garkuwarka da warwaji, * ka wo mani gudummuwar yaƙi.
Ka zaro mashinka da gatari, * don ka yi arangama da masu jan-daga da ni.
Ka gaya wa ruhuna cewa, * “ni ne nasararka.”
Masu neman raina, * bari su kunyata da ƙasƙanci.
Masu yi mani maƙarkashiya * su juya da kunya.
Su zama kamar ƙaiƙayi a gaban iska, * mala’ikan Yahweh yana tasa ƙeyarsu.
Bari ƙaddararsu ta zama Duhu da Hallaka, * mala’ikan Yahweh yana tangaza ƙeyarsu.
Gama a ɓoye sun gina mani rami, * sun ɗana tarko suna haƙon raina.
Bari Ramin ya ba su mamaki, * tarkonsu ya kama su, * su kuma fāɗa cikin ramin da suka gina.
Amma ruhuna zai yi murna da Yahweh, * ya ji daɗi cikin nasararsa.
Dukan ƙasusuwana za su ce, * “Yahweh, wa ke kama da kai?
Kā kuɓutad da gajiyye daga hannun wanda ya fi shi ƙarfi, * shi da mabukaci daga hannun mai
zaluntarsu.
Mashaidan ƙarya sun tayar mani, * waɗanda ban sani ba sun yi mani tambayoyi.
Sun saka mani alheri da mugunta, * suna baƙanta ruhuna.
Amma ni, lokacin da suka busa sarewa, * na sa tsumma.
Na hori kaina ta wurin azumi, * addu’ata ta liƙe a ƙirjina, * sai ka ce abokina ko kuma ɗan’uwa.
Ina tafiya kamar mai makokin mahaifiyarsa, * na dukufa da ɓakinciki.
Da na yi tuntuɓe, sai su fashe da dariya, * ’yan dambe sun kewaye ni.
Waɗanda ban sani ba suna ta yayyage ni, * ba su kuma dena yi mani ƙaraiyayi ba.
Masu ba’a kewaye da ni * suna ta murguɗa mani baki.
Ya Ubangiji, don me ka tsaya kana kallo kawai? * Ka ceci raina daga ramukansu * fuskata kuma daga kuyakuyan zakoki.
Zan gode maka a cikin babban taro, * a cikin babban biki ma zan yabe ka.
Kada magabtana masu ha’inci su yi murna a kaina, * ko ma magabtana masu limshe idanu.
Gama ba sa yin maganar salama, * amma suna afka wa marasa galibu na ƙasar.
Sun shirya makirci, * duk sun wage bakunansu a kaina.
Suna cewa, “Aha, Aha! * mun gan shi.”
Duba, Yahweh, kada ka yi shuru, * ya Ubangiji, kada ka yi nesa da ni.
Hanzarta ka zaburo don kāre ni, * ya Ubangijina da Allahna, ka taya ni fama.
Yahweh, ka kāre ni a cikin adalcinka, * ya Allah, kada ka bari su yi mani dariya,
ko su yi fahariya a cikin zukatansu, * su ce, “Haba, bakinmu ya kama shi,” * ko su ce, “Mun gama da shi.
Duk masu murna da rashin katarina, * bari su kunyata, su sha ƙasƙanci.
Duk masu shuka ƙarya a kaina, * bari a lulluɓe su da kunya da ƙasƙanci.
Amma duk masu son yin nasarata, * ka sa su yi sowa ta murna.
Su dinga cewa: * “Yahweh akbar!” * mai son zaman lafiyar bawansa.
Sannan ne halshena zai yi shelar adalcinka * in kuma yi yabonka dukan yini.
Zabura ta 36
Zunubi yana hura birnin zuciyar mugu, * baya ma fahimtar ma’anar tsoron Allah.
Amma Allahnsa zai hallaka shi da harara, * tun da yake ya ga saɓonsa.
Maganarsa cike take da miyagun ƙarairayi, * ƙetarsa tana hana shi tunani ko yin abin kirki.
Yana ƙaga mugunta a kan gadonsa, * kamin ya fita aikatata, * baya ma jin kunyar aikata kowane
mugun abu.
Yahweh, ƙaunarka daga sama take, * amincinka ya kai har cikin gajimarai.
Nagartarka ta milla sama kamar manyan duwatsu, * ƙaddararka tana da zurfi kamar teku.
Yahweh, kakan adana mutane da dabbobi, * alherinka akwai girma!
Alloli da mutane suna samun mafaka * a innuwar fukafukanka.
Suna biki da abinci mai kyau na gidanka, * kana shayar da su kuma daga kogin alherinka.
Kai ne tushen rai, * a cikin aljannarka za mu ga haske.
Ci gaba da ƙaunatar waɗanda suka san ka, * yi alheri ga masu zukatai nagari.
Kada ƙafar mai girman kai ta cim mani, * kada dantsen mugu ya yā da ni ƙasa.
Dubi yadda masu aikata mugunta ke faɗi, * sun fāɗi ƙasa warwas, ba su iya tashi.
Zabura ta 37
Kada ranka ya ɓaci saboda miyagu, * kada kuma ka ji haushin masu aikata sharri.
Domin sauran kaɗan za su bushe kamar ciyawa, * kamar ɗanyen ganye za su shuɗe.
Ka dogara ga Yahweh, ka aikata nagarta, * ka zauna a ƙasar, ka ci wadatarta.
Ka gamsu da Yahweh * zai kuwa biya maka bukatar zuciyarka.
Ka danƙa dabararka ga Yahweh, * ka dogara gare shi, zai kuwa cika ta.
Zai sa adalcinka ya haskaka kamar rana, * hakkinka kuma kamar tsakar rana.
Ka jira Yahweh, * ka sa zuciya gare shi.
Kada ranka ya ɓaci kan mutumin da ya arzuta, * yana nasara kan miyagun shirye-shiryensa.
Dena hushi, ka ya da harzuƙa, * kada ka cika damuwa, lahani kawai take jawowa.
Domin za a sassare miyagu, * amma tabbaci hakika masu kira da sunanYahweh za su gaji ƙasar.
Sauran kaɗan miyagu za su shuɗe, * in ka duba gidajensu, ba sa nan.
Amma gajiyayyu za su gaji ƙasar, * za su kuma ji daɗin albarka mai yawa.
Mugu yakan yi wa mai kirki maƙarƙashiya, * har yana cizon haƙora a kansa.
Ubangiji yana yi masa dariya, * domin ya ga ajalinsa yana gabatowa.
Miyagu suna zaro takobinsu, * suna ɗana baka
su ka da gajiyayyu da matalauta, * don su karkashe masu aikata gaskiya.
Takobinsu zai sassoki zukatansu, * bakanninsu kuma za su kakkarye.
Gara talaucin mai adalci * da wadatar mugu.
Domin wadatar miyagu zata rushe, * amma Yahweh zai tallafi masu gaskiya.
Yahweh yana lura da wadatar masu gaskiya, * gadonsu zai wanzu har abada.
Ba za su bushe a lokacin fari ba, * amma za su ƙoshi a kwanakin yunwa.
Amma miyagu za su yanƙwane, * magabtan Yahweh za su hallaka
kamar daji mai ƙonewa, * fiye da hayaƙi za su shuɗe.
Mugu yakan ci bashi, ya ƙi biya, * amma mai adalci yana bayaswa hannu sake.
Waɗanda ya sa wa albarka za su gaji ƙasar, * amma waɗanda ya la’anta sassare su za a yi.
Yahweh ne yake kare matakan mutun, * yana kuma tabbatad da tafiyarsa.
In ya kai hari ba za a yi takara da shi ba, * domin Yahweh yana ɗaga hannunsa.
Dā ni yaro ne, amma na tsufa, * tun da nike ban taɓa ganin inda aka ya da mai gaskiya ba, * ko kuma a ga ’ya’yansa na barar abinci.
A kullun yakan ba da rance hannu sake, * ’ya’yansu kuma albarka ce ke biye da su.
Rabu da mugunta, ka aikata alheri, * don ka wanzu har abada.
Domin Yahweh yana ƙaunar masu gaskiya, * baya kuma ya da masu bauta masa.
Za a hallaka miyagu, * ’ya’yansu ma za a sassare su.
Amma masu gaskiya za su gaji ƙasar, * su zauna cikinta har abada.
Bakin mai gaskiya yana maganar hikima, * halshensa ma na faɗar abin da ke daidai.
Shari’ar Allah na cikin zuciyarsa, * ƙafafunsa kuma ba za su yi tuntuɓe ba.
Da mugu ya makirci mai gaskiya, * yana neman kashe shi,
Yahweh ba zai sa shi a hannunsa ba, * ba ma zai bari a same shi da laifi ba in an tuhunce shi.
Ka jira Yahweh, * ka kiyaye hanyarsa,
domin zai ɗaga ka don ka mallaki ƙasar. * Za ka ga ran da za a sassare miyagu.
Na taɓa ganin mugu da wadata, * ya yi tsawo kamar ƙaƙƙarfan itacen al’ul.
Amma ya shuɗe, ba a ƙara ganinsa ba, * na nem shi, amma ba a iya samunsa.
Ka bi mala’ikan Kirki, ka dubi mala’ikan Gaskiya, * gama akwai albarka ga mutumin kirki.
Amma za a hallaka mutanen banza kwatakwata, * ba ma wata albarka da miyagu za su samu.
Daga wurin Yaweh ceton adalai yake, * shi ne mafakarsu a lokacin hari.
Yahweh ne zai kuɓutad da su, ya cece su, * zai fanso su daga hannun miyagu,
ya ba su kariya, * domin sun nemi mafaka a gunsa.
Zabura ta 38
Yahweh, kada ka tsananta mani loton hushinka, * kada ma ka hore ni da zafin hushinka.
Gama kibanka sun shisshige ni, * dantsenka kuma ya afko mani.
Ba lafiya a naman jikina, * saboda haushinka.
Ba ƙarfi a ƙasusuwana, * saboda zunubina.
Domin sharrin ƙetata ya dawo kaina, * kamar kaya mai nauyi ya danƙare ni.
Miyakuna suna zama gyambuna, suna ɗoyi, * don wawancina.
Duk na yanƙwane, ina kwance, * ina baƙinciki wuni zubut.
Domin jijiyoyina suna fama da zazzaɓi, * ba lafiya a naman jikina.
Na gaji, na tafke, * ina kururuwa da nishi a zuciyata.
Ya Ubangiji, duka ajiyar zuciyata tana gabanka, * kururuwata ba ta barin gabanka.
Zuciyata tana harbawa, * ba ni da ƙarfi.
Har ma ganin idanuna, * ya dushe.
Aminaina da abokan tafiya * sun kauce daga damuwata, * dangina sun yi nesa da ni.
Masu neman raina sun kafa mani tarko, * masu son ganin faɗuwata suna bina.
Bala’i da lalacewa * suke yi mani fata dukan yini.
Amma na yi kama da bebe da baya ji, * kamar kurma da baya magana.
Na zama kamar beben da baya ji, * wanda babu wata tsawatawa daga bakinsa.
Amma gare ka, Yahweh, kai ne nike jira, * Ubangijina da Allahna, ka amsa mani da nike cewa:
“Kada su yi murna a kaina, * kada su zage ni in na yi sassarfa.
Gama muguntata ta tsaya a kaina, * bakincikina yana gabana kullun.
I, ina rungume laifina a gabana, * ina firgita saboda zunubina.
Maƙiyana masu ƙarfi ne, * magabtana masu ha’inci suna da yawan gaske.
Masu rama mugunta da alheri * suna zagina, lokacin da nike nema masu alheri.
Yahweh, kada ka yashe ni, * ya Allahna, kada ka yi nesa da ni.
Ka gaggauta taimakona, * ya Ubangiji, ka cece ni!
Zabura ta 39
Na ce, “Zan yi hankali da abin da nike yi, * kada in kuskure da halshena.
Zan yi wa bakina linzami, * sa’ad da mugu ke yin surutu a gabana.”
Na yi shuru tsit, * na ƙi yin magana, * damuwata ta taso.
Zuciyata tana yi mani ƙuna, * in na yi tunani a kai, sai ka ce an cinna mani wuta.
Sai na yi magana, na ce, * “Yahweh, ka sanar da ni ƙarshena,
in san ko kwana nawa suka rage mani, * bari in san ajizancina.”
Ga shi, ka mai da rayuwata ’yar guntuwa, * shekaruna a gabanka kamar babu ne.
Kash! Kowa kamar hayaƙi ne, * kowane mutun siffa ne kawai.
Kash! Mutun kamar iska yake zagayawa. * Kash! Yana fusata a banza.
Yana jibge dukiya, * bai kuwa san mai cinta ba.
Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan roƙa, * Begena yana gare ka.
Daga dukan taurin kaina ka cece ni, * kada ka mai da ni gurbin wawa.
Na zama bebe, ban buɗe bakina ba, * ya Ubangiji, yi wani abu!
Ka kawar mani da bugunka, * domin kulkin hannunka zai hallaka ni.
Da tsawatawar laifin mutun kake horonsa, * kakan ci jikinsa kamar asu. * Kash! Kowane mutun
kamar iska ne.
Yahweh, ka ji addu’ata. * Ya Allah, ka saurari roƙona.
Kada ka zama bebe ga kwallana, * domin ni baƙo ne a gidanka, * mai ziyara kamar dukan kakannina.
Ka kau da fuskarka daga wajena don raina ya ji daɗi, * kafin in ƙaura, in dena wanzuwa.
Zabura ta 40
Na yi ta kiran Yahweh, * ya kuwa karkato gare ni, ya amsa kukana.
Ya tsamo ni daga Ramin Hallaka, * daga Lema Mai Caɓi.
Ya ɗora ƙafafuna a kan dutse, * na taka tudun-na-tsira.
Ya sanya sabuwar waƙa a bakina, * waƙar yabon Allahnmu.
Da yawa za su gani, su ji tsoro, * su ma dogara ga Yahweh.
Albarka ta tabbata ga mutumin * da ya dogara ga Yahweh,
bai juya ga gumaka ba, * ko ga siffofin ƙarya.
Yahweh, kā yi manyan ayyuka, * ya Allahna, kā aikata al’ajibai masu bammamaki.
Kana tunaninmu kullun, * ba wani kamarka.
Da na so in faɗe su duka, * sun fi gaban ƙidaya.
Ba ruwanka da hadaya ko baiko, * shi ya sa ka shirya kunnena ya ji.
Ƙonannen baiko da na gafarar zunubi * ba ka bukata.
Sannan na yi alkawali na ce, * “Ga shi, ina zuwa.
A cikin shafofin Littafi ne * aka rubuta wajibaina.
Ina jin daɗin aikata nufinka * ya Allahna, shari’arka tana cikin birnin zuciyata.”
Na bayyana albishir mai daɗi na cetonka * ga babban taron jama’a.
I, ban kulle leɓunana ba, * kai ma ka sani, Yahweh.
Ban rufe alherinka * a birnin zuciyata kaɗai ba.
Na bayyana amincinka * da aikinka mai ceto.
Ban ɓoye ƙaunarka * da amincinka ga babban taron ba.
Yahweh, kai ba ka hana ƙaunarka * zuwa gare ni ba.
Alherinka da amincinka * suna kiyaye ni a kullun.
Amma wahaloli sun kewaye ni, * har ba su ƙidayuwa.
Ƙaiƙan zunubaina ya komo mani, * har bana iya tsira.
Sun fi gashin kaina yawa, * zuciyata kuma ta karai.
Gaggauta, Yahweh, ka cece ni, * Yahweh ka yi hanzari ka taimake ni.
Bari dukan masu neman raina * su kunyata, su sha ƙasƙanci.
Duk masu neman kisa * su koma da kunya da ƙasƙanci.
Duk masu ce da ni, “Yauwa, yauwa!” * bari su karai don tseguminsu.
Bari dukan masu nemanka * su yi murna da farinciki a wurinka.
Bari dukan masu son cetonka * su yi ta cewa: “Yahweh akbar!”
Ko da nike gajiyayye da mabukaci, * Ubangiji zai tuna da ni.
Kai ne mataimakina, macecina, * ya Allahna, kada ka yi jinkiri.
Zabura ta 41
Albarka ga mai magana da azanci, * a lokacin hatsari Yahweh ya cece shi.
Yahweh ya kiyaye shi, ya tsawanta rayuwarsa, * ya yi masa albarka a duniya, * kada ya ba da shi ga magabtansa.
Yahweh ya tallabe shi a kan gadon jiyyarsa, * ka yi masa rangwame, * ka kau da ciwonsa.
Na ce, “Yahweh, ka ji tausayina, * ka warkad da ni, * ko da yake na yi maka laifi.
Magabtana suna zagina, suna cewa, * “Yaushe ne zai mutu, a manta da sunansa?”
In waninsu ya zo ya gaishe ni, * yana ƙaga ƙarya a zuciyarsa.
Yana tattara wa kansa ƙeta, * ya fita waje, yana tsegumguma.
Duk maƙiyana, ya Maɗaukaki, * suna raɗa da junansu a kaina, * suna shirya mani maƙarƙashiya, cewa:
“Zuba masa wani abu mai dafi, * domin wanda yake kwance kada ya sake tashi.”
Har ma abokina * wanda na amince da shi,
wanda muke ci a kushi ɗaya, * yana ƙulla ƙarairayi a kaina.
Amma kai, Yahweh, ka ji tausayina, * ka tashe ni, * domin in saka masu.
Sannan ne zan san kana sona, * in dai Magabcina bai yi rinjaye a kaina ba.
Saboda cikar kirkina ka sure ni, * ka aje ni a gabanka har abada.
Albarka ga Yahweh, Allah na Isra’ila, * tun fil’azal har abada abadin.
Amin. Amin.
Zabura ta 42
Kamar yadda kishimi ke kururuwa don ruwan rafi, * haka raina ke kururuwa gare ka, Allah.
Raina yana jin ƙishi, * Allah, ya rayayyen Allah.
Yaushe ne zan soma sha * a gaban fuskar Allah?
Hawayena sun zama abincina * dare da rana,
a kullun kuma ana tambayata, * “Ina Allahnka?”
Waɗannan abubuwa nike tunawa, * zan zubar da ruhuna gare shi
in na ƙetare dokin ƙofa, * in na kwanta rub da ciki * kusa da gidan Allah,
inda ake yin sowar ta yabon Allah, * tare da taron alhazan Ƙudus.
Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?
Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna
Zuciyata ta karaya, * Maɗaukakin Zati, ina tunawa da kai
daga Magangaran Lahira duk da tarunanta, * daga gindin dutsenta.
A can ruwa mai zurfi ke kiran ruwa mai zurfi, * yana amsa wa tsawarka.
Dukan raƙuman ruwanka masu husata * suna taɗiye ni.
Dā Yahweh yakan aiko mani da alherinsa da rana, * da ru’yarsa kuma da dare.
Ina yin addu’a ga Allahna rayayye, * ina cewa, “ya Allah, Dutsena,
me ya sa ka mance da ni? * Me ya sa nike sha takaici
saboda matsawar Magabci, * saboda Makashin cikin ƙasusuwana?”
Maƙiyana suna bakanta mani, * a kullun suna cewa da ni, * “Ina Allahnka?”
Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?
Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna
(Zabura ta 43)
Ka kāre ni, ya Allah, * ka tsaya wa hakkina.
Ka fanshe ni daga hannun marasa bin Allah, * daga hannun mayaudara, marasa gaskiya.
Tun da kai ne Allah Mafakata, * me ya sa ka yā da ni?
Dom me nike shan takaici * saboda matsawar Magabci?
Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, * i, bari su yi mani jagora.
Bari su kai ni zuwa dutsenka mai tsarki * wurin zamanka.
Bari in tafi wurin bagaden Allah, * gun Allah, mai faranta mani rai.
Bari in yabe ka da garaya, * ya Allah, Allahna.
Me ya sa kake ɓaci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?
Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna.
Zabura ta 44
Ya Allah, mun ji da kunnuwanmu,* kakanninmu sun gaya mana
ayyukan da ka yi a zamaninsu, * a zamanin dā hannunka ya aikata al’ajibai.
Kā kori sauran al’ummai, * amma kā dasa taka.
Kā warwatsa sauran kabilu, * amma kā sa taka ta yi toho.
Ba da kaifin takobinsa suka ci ƙasar ba, * ba da ƙarfin dantsensu suka yi nasara ba,
amma ta hannun damanka da dantsenka ne * da hasken fuskarka, * tun da yake ka ƙaunace su.
Kai ne Sarkina, Allahna, * Shugabana, Macecin Yakubu.
Ta wurinka mun fatattaki abokan gabanmu, * ta sunanka muka tattaka masu nemanmu da yaƙi.
Domin ban dogara ga bakana ba, * takobina kuma bai sa in ci nasara ba.
Amma ka sa mun yi nasara kan abokan gabanmu, * ka kuma kunyata maƙiyanmu.
Da Allah ne muke yin taƙama kullun, * sunanka ne kuma za mu yaba har abada.
Amma ka yi watsi da mu, ka ƙasƙantad da mu, * ba ka kuma ƙara taya sojojimu ba.
Ka sa abokan gabanmu su ga ƙeyarmu, * maƙiyanmu kuma sun ƙwace kayanmu.
Ka bashe mu kamar bisashen da za a yanyanka, * ka warwatsa mu a cikin al’ummai.
Ka sayar da mutanenka arha, * ba su yi tsada ba.
Ka mai da mu abin zagi ga maƙwabtanmu, * abin reni da ba’a ga waɗanda ke kewaye da mu.
Ka mai da mu abin zunɗe ga al’ummai, * abin kaɗa kai ga mutane.
Wulakancina yana gabana kullun, * kullun ina sane da kunyata,
saboda muryar mai zagin nan da mai saɓon nan, * saboda magabci da mai neman ramuwa.
Kowane wulakanci ya zo mana, * amma ba mu mance da kai ba, * ko yin rashin biyayya da yarjejeniyarka.
Zuciyarmu ba ta juya baya ba, * ƙafafunmu kuma ba su goce daga hanyarka ba,
ko da yake ka wahalshe mu da ciwon gindi, * ka ma rufe mu da duhu baƙiƙ ƙirin.
In da mun mance da sunan Allahnmu, * ko mun miƙa hannu ga wani allah,
ashe Allah ba zai tona wannan ba? * tun da yake ya san lungu-lungu na zuciya.
Duk da haka, saboda kai ne ake kashe mu yini zubut, * ana ƙirga mu kamar tumakin da za a yanka.
Ka farka! Dom me kake barci, ya Ubangiji, * ka tashi, kada ka yi hushi, ya Jarumi.
Me ya sa ka kau da fuskarka, * ka mance da ƙuncinmu da danniyar da ake yi mana?
Domin wūyanmu ya bunkuya cikin turɓaya, * cikinmu ya nane ƙasa.
Ka tashi, ka agaje mu, * ka fanshe mu saboda ƙaunarka.
Zabura ta 45
Zuciyata ta wallafa waƙa mai daɗi, * zan raira aikina, ya Sarki,
halshena alkalamin ƙwararren marubici ne.
Kai ne mafi kyau a cikin dukan ’yan’adan, * daɗɗaɗar magana na fitowa daga leɓunanka.
Allah, Maɗaukakin Zati, * ya albarkace ka tun fil’azal.
Ka ɗora takobinka a kan cinyarka, * ka rinjaya da darajarka, * ka ci nasara da sarautarka.
Ka rinjaya a harinka saboda gaskiya, * ka ma kāre matalauta.
Al’ajiban hannunka na dama da kibanka masu tsini * su za su sa ka yi suna.
Al’ummai za su fāɗi a gabanka, * magabtan Sarki su kwanta sumammu.
Allah Madauwami ya tabbatar da sarautarka, * sandar sarautarka sanda ce ta gaskiya.
Ƙaunaci gaskiya, ka ƙi mugunta, * Madauwamin Zati ya shafe ka, * Allah, Allahnka.
Mayafanka ne man farinciki, * duk tufafinka su ne mur da aloyes da tafasa.
Ai, akwai gidajen hauren giwa barkatai, * don faranta maka zuciya.
’Ya’yan sarakuna mata na cikin matan fādarka, * sarauniya na tsaye a hannun damanka da kayan zinarya ta Ofir.
Saurara, ke ɗiya, ki gani, * ki kasa kunne: * Manta da mutanenki * da gidan mahaifinki.
Domin Sarki yana marmarin kyanki, * i, shi ne ubangijinki, * ki yi masa sujada.
Riga daga garin Taya tana a cikin kyautayinki, * manyan baƙi ma suna biɗar alherinki.
Dukan tufafinta iri na sarauta ne, * a ciki an yi masu dajiya da zinariya, * gwanayen maɗinka ne suka yi kayanta.
Bari a kai Gimbiya wurin Sarki, * daga baya kawayenta su bi.
Ku zo, bari a raka ta da murna da farinciki, * a shigar da ita fādar Sarki.
Gurbin kakanninka ’ya’yanka za su maye, * za ka maishe su sarakunan dukan duniya.
Zan yi shelar sunanka a dukan zamanai, * dukan jama’a za su yabe ka, ya Maɗaukaki Madauwamin Zati.
Zabura ta 46
Allah ne maɓoyarmu da mafakarmu, * Mai Duka, mun same shi Macecinmu daga yaƙi.
Maɗaukakin Zati, ba za mu ji tsoron * muƙamuƙan Ƙalƙashin Ƙasa ba.
Ko faɗawar duwatsu * a tsakiyar teku,
ko da ruwayen teku na kumfa, * duwatsu na fāɗuwa cikinsu, * igiyoyin ruwa suna gilme-gilme.
Allah yana kawo wa birninsa farinciki, * Maɗaukaki yana tsarkake mazauninsa.
Da yake Allah na cikinsa, * ba zai girgiza ba.
Zai taimake shi * tun da asuba.
Al’ummai sun raunana, * sarautu sun jijjigu.
Ya yi furci, * duniya ta narke.
Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.
Ku zo, ku ga ayyukan Yahweh, * wanda ya sa wa duniya albarka.
Yakan tsaid da yaƙi * har bangon duniya.
Ya kan karya baka, yana lalata mashi, * yana ƙone karusai da walƙiya.
Ku kwantar da hankalinku, ku sansance ni ne Allah, * ina bisa al’ummai, * na ma mallaki duniya.
Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.
Zabura ta 47
Dukanku ƙafarfan ruhuna, ku yi tafi, * ku alloki, ku yi sowa ta murna.
Yahweh Maɗaukaki mai ban tsoro ne, * babban sarki ne bisa dukan duniya.
Ya bi mana da mutane, * ya sa al’ummai a ƙalƙashen ƙafafunmu.
Ya zaɓi mulkinmu don kansa, * ƙasar Yakubu abar taƙama da yake ƙauna.
Allah ya hau da sowa, * Yahweh da muryar kakaki.
Ku raira yabbai, ku alloki, ku raira yabbai, * ku raira yabbai ga Sarkinmu, ku raira yabbai.
Gama shi ne Sarkin dukan duniya, * ku alloli, ku raira yabo da gwaninta.
Allah ne ke mulkin al’ummai, * yana zaune kan tsattsarkan kursiyinsa, * ku sarakunan jama’a, ku tattaru.
Allahn Ibrahim Mai Iko ne, * Allah shi ne Mai duniya, * shi ne kuma mafi dacewa da ɗaukaka.
Zabura ta 48
Yahweh mai girma ne, * ya cancanci matuƙar yabo.
A birnin Allahnmu * akwai tsattsarkan dutsensa.
Ƙololuwa mai kyan gani, * da ke faranta wa dukan duniya rai,
Dutsen Sihiyona ne babban birnin duniya, * birnin Sarki mai girma.
Karagarsa Allah ne * da gwadajjiyar mafaka.
Gama sarakunan sun taru, * sun kai hari tare.
Da suka ga garin sun yi mamaki, * suka firgita, suka ranta a noman kare.
Tsoro ya kama su * i, azaba kamar ta mace mai naƙuda,
kamar yadda iskar gabas * kan kakkarya jiragen ruwan Tarshishi.
Kamar yadd muka ji, * haka muka gani
a birnin Yahweh mai runduna, * a birnin Allahnmu.
Allah zai tabbatad da shi * har abada abadin.
Mun tuna da ƙaunarka, ya Allah, *a tsakkiyar Haikalinka.
Kamar sammanka, ya Allah, * haka yabonka ke kaiwa har bangon duniya.
Hannun damanka cike yake da alheri, * bari dutsen Sihiyona ya yi murna,
ƙauyukan Yahuda kuma su yi farinciki, * saboda ayyukanka na tsare su.
Ku zaga Sihiyona, ku kewaye ta, * ku ƙirga hasumiyoyinta.
Ku dubi ganuwarta, * ku binciki ginin tsaronta,
donin ku gaya wa tsara mai zuwa, * cewa “Birnin nan na Allah ne.”
Madauwamin Allahnmu * shi zai bishe mu har abada.
Zabura ta 49
Ku ji wannan, ku dukan jama’a. * Ku saurara, ku dukan mazauna duniya,
ƙasƙantattu da ɗaukakakku, * mawadata da matalauta duka.
Bakina zai yi zancen hikima, * zuciyata za ta furta fahinta.
Zan kasa kunnena ga misali, * zan raɗa kacinci-kacincina da kiɗin molo.
Don me zan ji tsoron miyagun kwanaki, * ko ƙetar maƙaryata kewaye da ni,
waɗanda ke dogara ga dukiyarsu, * suke fahariya da ɗumbin wadatarsu?
Kai! Mutun baya iya ceton kansa, * ko ya biya wa Allah fansarsa.
Gidan Can Ƙasa zai zama fansar ransa, * zai tafi har abada,
ko da yake dā ya iya rayuwa da murna har abada, * da ma bai ga Ramin ba.
In Allah ya fuskanci masu hikima, za su mutu. * In ya harari wawaye,
nan da nan za su hallaka, * su bar wa wasu dukiyarsu.
Loton da suke a madauwamin gidansu, * mazauninsu na har abada,
magadansu a duniya * suna ambaton sunayensu.
A Gidan Ƙasa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka shuɗe.
Wannan ce ƙadarar mawadata, * da ƙarshen masu mugun kwaɗayi.
Tamkar bisashe za a jefa su a Shawol, * Mutuwa ce za ta zama mai kiwonsu.
Za su gangara cikin maƙogwaronta kamar ɗan maraƙi, * Shawol za ta haɗiye gaɓoɓinsu, * Mai Cinyewa zai gama da su.
Amma Allah zai fanshe ni, * ba shakka zai kwato ni daga hannun Shawol.
Kada ka yi ƙyashin mai arziki, * lokacin da wadatar gidansa ke haɓɓaka.
Domin lokacin da ya mutu ba zai tafi da kome ba, * dukiyarsa ba za ta bi shi ba, * ko da ya bauta wa sha’awarsa lokacin da yake da rai.
Duk da ana yabonka in ka arzuta, * za ka shiga taron kakanninka, * waɗanda ba za su ƙara ganin
haske ba.
A Gidan Ƙasa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka
shuɗe.
Zabura ta 50
Allahn alloli shi ne Yahweh, * ya yi magana, ya kirayi duniya, * daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.
Daga Sihiyona, cikamakin kyau, * Allah ya hasko.
Allahnmu yana zuwa, * ba zai yi shuru ba.
Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, * kewaye da shi kuma da hadari mai tsawa.
Ya kirayi sama da ƙasa * wajen shari’ar jama’arsa.
Ku tattaro masa masu yi masa bauta, * masu jarjejeniya da shi a gaban hadaya.
Bari sammai su yi shelar hakkinsa, * domin shi ne Allah mai gaskiya.
“Ku saurara, jama’ata, zan yi magana, * Isra’ila kam, zan yi magana mai gāba da ke. * Ni ne Allah, Allahnki.
Ban tsauta maki saboda hadayunki ba, * ko hadayun ƙonawarki da ke gabana kullun.
Ban biɗi bajimin sa daga gidajenku ba, * ko awaki daga garkunanku,
tun da yake dukan namomin daji nawa ne, * da dabbobin da ke bisa duwatsu.
Na ma san dukan tsuntsayen da ke kan duwatsu, * duk mai yawon karkara ma a gabana yake.
Da na ji yunwa, da ba zan gaya maku ba, * domin duniya tawa ce da dukan abin da ke cikinta.
Ina cin naman bajimai, * ko in sha jinin awaki?
Miƙa wa Allah hadayarka ta godiya, * ka cika wa’adodinku ga Maɗaukaki.
Sannan ka kira ni a lokacin wahala, * zan cece ka, in kira ka biki.”
Amma game da mugu Allah ya ce: * “Ta yaya za ka furta dokokina, * ka ambaci yarjejeniyata da bakinka?
Tun da yake ba ka son a koya maka, * kana kuma yin watsi da kalmomina.
Lokacin da ka ga ɓarawo, kana yin gasa da shi, * kana kuma cudanya da mazinata.
Da bakinka kake furta mugunta, * da halshenka kake saƙa yaudara.
Ka zauna kana yin gulma da ƙanenka, * kana yaɗa aibu ga ɗan mahaifiyarka.
Duk ka yi waɗannan abubuwa, * to, ni zan yi shuru ne?
Kā shirya makirce-makirce, * ni ma kamarka ne?
Zan tuhume ku, in gabatad da ƙara * a gaban idanunka.
Ku yi tunani kan wannan, ku da ke mance wa Allah, * kada in cafke ku, ba mai ƙwacewa.
Duk wanda ya miƙa hadayar yabo, * zan gayyace shi biki.
Wanda ya tsaya a kan hanyata, * zan shanyad da shi sosai da ceton Allah.”
Zabura ta 51
Ka ji tausayina, ya Allah, * saboda ƙaunarka.
Saboda yawan rahamarka, * ka shafe tawayena.
Zubo ruwa, ka wanke ni daga muguntata, * ka tsarkake ni daga zunubaina.
Sharrin ƙeta da ke tuhumata na san shi, * zunubina gabana yake kullun.
Kai kaɗai ne na yi wa laifi, * na yi zunubin nan a idanunka.
To, ka yi daidai a shari’ar da ka yanke, * hukuncin da kakan yi ba shi da aibu.
I, da laifi aka ɗauki cikina, * ni mai zunubi ne tun haifuwata.
I, ka fi son gaskiya * fiye da sanin boka da wayon wulli, * ka koya mani hikima.
Ka raba ni da zunubi, * zan kuma tsarkaka fiye da ruwan ƙalƙashin dutse, * ka wanke ni, zan fi auduga fari.
Bari in ji farinciki da murna, * bari ƙasusuwan da aka rumurmutse su farfaɗo.
Ka kau da fuskarka daga zunubaina, * ka shafe dukan ƙetata.
Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, * ka sa mani sabon ruhu na biyayya.
Kada ka kore ni daga gabanka, * ko ka ƙwace mani Ruhunka Mai Tsarki.
Ka mayar mani da farinciki na cetonka, * ka ƙarfafa ni da ruhun biyayya,
domin in koya wa masu tawaye hanyoyinka, * masu zunubi kuma za su juyo gare ka.
Ka cece ni daga ƙwallan mutuwa, * ya Allah, Allahna.
Sannan ne, Macecina, * halshena zai raira yabon alherinka da ƙarfi.
Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, * halshena kuma zai furta yabonka.
Da ka so hadaya, * da na miƙa, * da ka yi marmarin hadaya ta ƙonawa, da na bayas.
Hadaya mafi kyau, ita ce ruhu na ƙasƙanci, * ƙasƙantaciyyar zuciya, ya Allah, ba za ka yas ba.
Ka sabunta kyan Sihiyona da alherinka, * ka sake ginin ganuwar Urushalima.
Sannan ne za ka karɓi hadayun da ke daidai, * ƙonannun hadayu, * har ’yan marƙa za su hau bagadinka.
Zabura ta 52
Don me kake alfari da ƙeta, kai gawurtaccen mutun? * Mai bautar Allah, me ya sa ka ke tunanin fitina kullun?
Halshenka kamar kakkaifar aska yake, * ya kai gwanin yaudara.
Ka fi son mugunta da nagarta, * da ƙarya maimakon faɗin gaskiya.
Kana ƙaunar dukan batutuwa * da halshenka mai yaudara ke yi.
Allah ya hana ka haifuwa har abada, * ya rushe ka da tsawa!
Ya koro ka daga alfarwarka, * ya janye rayukan ’ya’yanka daga duniya.
Masu gaskiya za su duba da tsoro, * amma daga baya za su yi masa dariya, su ce:
“Ga mutumin nan * da bai mai da Allah mafakarsa ba,
amma ya dogara ga yawan wadatarsa, * ya dogara ga mugun abunsa.
Ni dai, kamar itacen zaitun ne, * da ke girma a cikin gidan Allah,
na dogara ga ƙauna * ta Madauwamin Allah.
Ina yabonka, ya Madauwami, * domin ka aikata.
Zan yabi sunanka * mai daɗi gun masu bauta maka.
Zabura ta 53
Wawa yana tunani a zuciyarsa, * cewa, “Allah baya nan.”
Masu ha’inci ne, suna yin miyagun abubuwa, * babu wani mai aikata alheri.
Daga sama Allah yana dubo * dukan ’yan’adan,
ya gani ko akwai masu hikima, * da ke neman Allah.
Amma dukansu sun bauɗe, * duk miyagu ne.
Babu mai yin kirki a cikinsu, * ko mutun ɗaya.
Masu aikata aibu ba su sani ba, * in sun washe jama’arsa,
suna cin hatsin Allah, * wanda ba su yi girbi ba?
Ga yadda suka yi ƙungiya ta sojinsu, * amma hari bai daɗe ba,
domin Allah ya yi kaca-kaca * da ƙasusuwan masu kai maku hari.
Kun karai * sai da Allah ya tara gawarwakinsu.
Daga Sihiyona wa zai kawo wa Isra’ila ceto? * Lokacin da Allah ya sake arzuta jama’arsa,
bari ’ya’yan Yakubu su yi farinciki, * ’ya’yan Isra’ila su yi murna.
Zabura ta 54
Ya Allah, ka cece ni da sunanka, * ta ikonka kuma ka kāre ni.
Ya Allah, ka ji addu’ata, * ka kasa kunne ga kalmomin bakina,
domin baƙi sun tasam mani, * ’yan iska suna neman raina, * ba su san Allah shugabana ba ne.
Dubi yadda Allah ya zama mataimakina, * Ubangiji Matallafin raina.
Ya saka wa masu ɓata mani suna da muguntarsu, * da amincinsa ya hallaka su.
Saboda darajarka zan yi maka hadaya, * Yahweh, zan yabi sunanka mafificin kyau.
Gama ya tserad da ni daga dukan maƙiyana, * idanuna sun ga yadda ya yi nasara da magabtana.
Zabura ta 55
Ya Allah, ka ji addu’ata, * kada ka zama kurma ga roƙona.
Ka karkato gare ni, ka amsa mani, * ka sauko inda ni ke ƙara.
Na gigice da muryar abokin gaba, * da hararar miyagu,
domin suna tila mani zage, * suna ci mani fuska.
Zuciyata tana raɗaɗi a cikina, * razanar mutuwa tana girgiza ni.
Tsoro da fargaba sun afka mani, * sai makyarkyata nike yi.
Sai na ce, “Wa zai ba ni fukafukai kamar na kuruciya, * don in tashi fir in huta.
Da sai in tafi nesa, * in sauka a kungarmin daji.
Zan hanzarta zuwa mafakata, * daga iska mai ƙarfi da hadari.”
Ya Ubangiji, ka hallaka halshensu mai rinto, * domin na ga tashin hankali da hargitsi a cikin birnin.
Dare da rana suna kewaye da shi. * A kan garunsa akwai ƙeta da fitina.
Daga tsakkiyarsa ayyukan mugunta suna fitowa, * daga tsakkiyarsa ba su dena zuwa ba, * daga dandalinsa zalunci da zamɓa suna watsuwa.
Ba magabci ba ne * wanda ya yi mani cin fuskar da nike jurewa.
Ba maƙiyi ba ne ya ɓata mani suna, * balle in ɓuya daga gare shi.
Amma kai ne, aminina, * abokina da na amince da shi.
Mun saba yin shirin zaune tare * a cikin Gidan Allah, * inda muke cudanya da taron jama’a.
Bari mutuwa ta afko masu, * bari su gangara Shawol da ransu,
domin magana mai dafi na fitowa * daga maƙogwaronsu da ƙirjinsu.
Amma na yi kira ga Allah, * Yahweh kuwa ya cece ni.
Da yamma, da safe, da rana tsaka * ina kai ƙara da nishi.
Mafanshi kuwa ya ji muryata, * yana biyan kuɗin raina.
Ya matso kusa da ni * lokacin da masu yawa suke gāba da ni.
Allah ya ji ni, * Mai Zamanu ya ba ni amsa, * domin ba canzawa a gare shi.
Duk da haka, basu da tsoron Allah. * Wancan mutun ya sa hannu kan amininsa, * ya saɓa yarjejeniyarsa.
Maganarsa ta fi kitse taushi, * amma zuciyarsa tana cike da ƙiyayya.
Kalmominsa sun fi mai sulɓi, * amma a gaskiya sun fi takobi kaifi.
Yahweh Maɗaukaki ne Mai Arzutaka, * Mai Ba ka wanda ke tallafa maka.
Har abada ba zai bar * mai gaskiya ya yi tuntuɓe ba.
Amma kai, ya Allah, za ka kai su, * Rami mai Caɓi.
Kada masu gumaki da tsafi * su rayu rabin kwanakinsu. * Amma ni, na dogara gare ka.
Zabura ta 56
Wuni zubut * suna tozarta ni da muƙamuƙansu.
Masu yankena suna wahalda ni wuni zubut, * mutane barkatai ne ke yaƙi da ni.
Ya Maɗaukaki, in na firgita, * ina dogara gare ka.
Da Allah nike taƙamai, kai mai yanke! * Na dogara ga Allah.
Bana jin tsoro. * Me mutun zai iya yi mani?
Wuni zubut masu yankena suna harzuka ni, * suna mugun shiri a kaina kullun.
Suna shawara da juna da mugun nufi a asirce, * dubi yadda masu kushena ke kallo, * kamar tarkon ƙafa suke neman raina.
Ka cece mu daga ƙetarsu, * cikin hushinka ka tsawata wa al’ummai, ya Allah!
Ka rubuta makokina kai da kanka, * ka lissafta hawayena a kan takardarka, * da gajiyata a ckikin kundinka.
Da magabtana sun juya, * sun yi dabur-dabur da na yi kira,
sannan nike sani, * lalle Allah yana goyon bayana.
Da Allah ne nike taƙama, kai mai yanke! * Da Yahweh nike taƙama, kai mai yanke!
Na dogara ga Allah. * Bana jin tsoro. * Menene mutun zai iya yi mani?
Hakika, ya Allah Maɗaukaki, * zan biya wa’adodina * tare da yabbanka.
Sai ka cece ni daga Mutuwa, * ka hana ƙafafuna zuwa cikin Kora,
domin in yi tafiya a gaban Allah * a cikin aljannar rayuwa.
Zabura ta 57
Ka tausaya mani, ya Allah, ka tausaya mani, * domin a gare ka nike fakewa.
A innuwar fukafukanka nike fakewa, * har bala’in nan ya wuce.
Ina kira ga Allah Maɗaukaki, * ga Allah, Sarkin Sakayya.
Zai aiko daga sama a cece ni, * daga cin mutuncin masu tozarta ni.
Allah zai aiko * da alherinsa da amincinsa.
Ina kwance a tsakkiyar zakoki, * ga shi, suna marmarin naman ’yan’adan.
Haƙoransu masu ne da kibau, * harsunansu takubba ne masu shegen kaifi.
Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ɗaukakarka ta rufe dukan duniya.
Sun haƙa wa ƙafafuna tarko, * da igiya don su zarge wuyana.
Sun gina rami don in fāda ciki da kā, * da ma su yi kundumbala a ciki.
Na shirya zuciyata, ya Allah, * na shirya zuciyata, * zan yi waƙa in yabe ka.
Ki farka, zuciyata! * Ku farka, molona da garayata! * Sai in farkad da asuba!
Zan gode maka a cikin jama’a, ya Ubangiji, * zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Mai Duka.
Domin alherinka ya kere sammai, * amincinka kuma ya zarce sararin sama.
Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ɗaukakarka ta rufe dukan duniya.
Zabura ta 58
Ya ku mashawarta, ku alkalai, ku zartad da hukuncin adalci, * ku yi mulkin ’yan’adan da gaskiya.
Amma ba haka ba, kuna aikata ƙeta a zukatanku, * da zalunci kuke yanke shari’a ta son ranku.
Miyagu abin ƙyama ne tun daga ɗaukar cikinsu, * tun daga haifuwa maƙaryata ke bauɗewa.
Dafinsu kamar na maciji ne, * suna yin kama da kububuwa mai tosasshen kunne,
wadda ba ta jin muryar gardawa, * ko ta gwanayen tsibbu.
Ya Allah, ka zub da haƙoransu daga bakunansu, * Yahweh, ka kakkarya fiƙoƙin kuyakuyan zakoki.
Bari su zube, kamar ruwa mai gudu, * su ɗana kibansu ba tare da ƙarfin harbi ba.
Kamar wanda ciwon ƙanjamau ya takure, bari ya ƙaura * kamar ɓarin mace, kada su ga hasken rana.
Kafin su yi la’akari da hadarinka, * bari zafin haushinka ya watsad da su.
Mai adalci zai yi murna in ya ga nasararsa, * zai wanke ƙafafunsa daga jinin miyagu.
Mutane za su ce, “Zama mai adalci abin kirki ne. * Hakika akwai Allah mai shara’anta duniya!”
Zabura ta 59
Ka cece ni daga abokan gabata, ya Allah, * a game da masu tasar mani ka zama ganuwata!
Ka cece ni daga masu aikata mugunta, * daga masu gumaka ka fanshe ni.
Dubi yadda suke fakon raina, * masu iko suna yi mani maƙarƙashiya.
Ba don laifina ba, * ba don zunubina ba, Yahweh,
ba don kurena ba, * sun sha mani da-ga.
Tashi, ka bi ni, * ka gani da kanka,
Yahweh, Allah mai runduna, * Allah na Isra’ila.
Farka domin ka hori dukan al’ummai, * kada ka ji tausayin miyagun masu ha’inci.
Sukan dakata sai maraice, * kāna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.
Duba daga bakunansu da leɓunansu suna aman takubba. * Suna cewa, “Wanene zai saurare mu?”
Amma, Yahweh, za ka yi masu dariya, * kana mai da dukan al’ummai abin wasa.
Allahna mafakata ne, * hakika ina samun kariya.
Allah, shi ne ganuwata, * hakika Allah ne katangata.
Allah zai riga ni zuwa, * zai sa in yi wa magabtana dariya.
Ya Allah, ka kashe su, * kada mutanena su razana.
Ka runtume su daga mafakarka, * ka yā da su ƙasa, * ya Ubangiji Shugabanmu.
Bari a kama su ta zunubin bakinsu * da gulmar leɓunansu.
Saboda izgilancinsu, zage-zage da ƙarairayinsu, * bari a shafe su.
Ka hallaka su da hushinka, * ka hallaka, ka shafe su,
domin su sani Allah ne * yake mulki daga ƙasar Yakubu * har zuwa bangon duniya.
Sukan dakata sai maraice, * kāna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.
Da haushi sukan nemi rabonsu, * in ba su ƙoshi ba, sai su ci gaba.
Zan yi waƙar ikonka, * kowace safiya zan yabi ƙarfinka,
domin kā zama ganuwata, * da katangata lokacin hari.
Allah mafakata ne, * hakika yana tsare ni.
Allah shi ne ganuwata, * Allah ne katangata.
Zabura ta 60
Ya Allah, ka ji hushi da mu, ka guje mu. * Kā yi haushi, ka juya mana baya.
Kā girgiza ƙasar, ta kuwa rugurguje.* Raunanniya daga targaɗenta, * ta gigice sosai.
Kā sa jama’arka su shanye ƙoƙon, * kā sa mun sha abinshan inabi da ya bugar da mu.
Ka ba masu tsoronka tuta, * inda za su iya gāba da masu baka.
Domin ka kuɓutad da ƙaunatattunka, * da hannun damanka sa mu yi rinjaye, mu ci nasara.
Allah ya yi magana daga tsattsarkan gidansa, ya ce: * “Ku ji, zan raba Shekem, * in auna kwarin Sukkot.
Gileyad nawa ne, har da Manassa, * Ifraimu hulata ne, * Yahuda kuma sandata ce ta sarauta.
Mowab bangajin wankina ne, * a kan Edom zan taka da takalmina, * a kan Filistiya zan yi ihun nasara.
Wa zai kai ni Birnin Dutse? * Wa zai ba ni gadon Edom?
Amma kai, ya Allah, za ka yi hushi da mu? * ba za ka ƙara fita da sojojinmu ba?
Ka ba mu ’yanci daga abokan gaba, * tun da yake taimakon mutane banza ne.
Da ikon Allah za mu yi nasara, * shi kansa ne zai tattake magabtanmu.
Zabura ta 61
Ya Allah, ka ji kukana, * ka saurari addu’ata.
Daga bakin Ƙalƙashin Ƙasa * na yi kiranka, * lokacin da zuciyata ta karaya.
Ka jawo ni daga bakin Ramin * zuwa Dogon Dutse.
I, zama mafakata, * hasumiyar tsaro daga Magabcina.
Bari in zauna a madauwamiyar alfarwarka, * in sami tsira a innuwar fukafukanka.
Ya Allah, ka ji wa’adonina, * ka biya begen mai tsoron sunanka.
Ka ƙara shekaru ga shekarun sarki, * shekarunsa su zama tsararraki barkatai.
Bari ya zauna kan kursiyinsa a gaban Allah har abada, * ka sa alheri da aminci su kiyaye shi.
Sannan zan yi waƙar sunanka har abada, * ina cika wa’adodina kowace rana.
Zabura ta 62
Allah mai alloli, * shi kaɗai ne mafakata. * Ya raina, daga gare shi ne cetona zai zo.
Shi kaɗai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan fāda a Tarun ba.
Don me za ku dinga maganar banza, * kuna ta yin tsegumi a kan mutun?
Dukanku kama da bango mai son fāɗi, * ko dangar da ta kishingiɗa.
Yauɗara ce kawai suka runguma, * suna jin daɗin ƙarairayi.
I, da baka suna sa albarka, * amma a zuci suna yi maka la’ana.
Allah kaɗai ne mafakata,* ya raina, daga gareshi ne nike samun bege.
Shi kaɗai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan yi tuntuɓe ba.
Allah Maɗaukaki ne nasarata, * Mai Ɗaukaka shi ne mafakata, * Allah shi ne masterata.
Ku dogara gare shi, Mai Iko ne kullun, * ku buɗe zukatanku gare shi, * domin Allah ne matseranmu.
Talakawa kamkar hayaƙi suke, * manyan mutane kuma kamar tururi.
A kan sikelai ba su yi nauyin ganyaye ba, * dukansu biyu kuma ba su kai nauyin iska ba.
Kada ku cika rungumar zulunci, * kada ku mai da dukiya gunkinku.
In Allah ya yi magana, * ku saurara.
Abu ɗaya ne Allah ya faɗi, * biyu kaɗai ne na ji:
“Iko na Allah ne, * a gare ka kuma, ya Ubangiji, ƙauna take.
Domin kana saka wa kowane mutun * gwargwadon aikinsa.
Zabura ta 63
Ya Allah, Allahna, * kai ne nike marmari.
Raina yana jin ƙishinka, * jikina na begenka,
fiye da yadda busasshiyar ƙasa * ke marmarin ruwa.
A tsattsarkan mabautarka bari in zuba ido gare ka, * ina kallon ikonka da ɗaukakarka.
Domin ƙaunarka tana da daɗi * fiye da rayuwata da leɓunana da ke yabonka.
A madauwamiyar rayuwata ka sa in yabe ka, * a samaniyarka kuma in ɗaga hannuwana zuwa gare ka.
A can zan yi biki, in ƙoshi * da madara da man shanu.
Leɓunana za su yi sowa ta murna, * bakina kuma zai raira yabonka.
A kan gadona ina tunawa da kai, * dukan dare ina tunaninka.
Ka zama Mataimakina! * Bari in ɓuya a cikin innuwar fukafukanka.
Bari in manne maka, * hannunka na dama kuwa ya ɗaga ni.
Amma masu neman kisana, * bari su tafi can ƙurewar Ƙalƙashin Ƙasa.
Bari su gamu da kaifin takobinsa, * duk su zama kalacin kyarketai.
Sarki zai yi murna da Allah. * Duk wanda ya rantse da shi zai gama lafiya, * amma za a toshe bakin maƙaryata.
Zabura ta 64
Ka kiyaye raina daga taron maƙiya, * ka ɓoye ni daga miyagun mashawarta, * daga rukunin ’yan iska,
masu wasa halshensu kamar takobi, * suna bārā da maganarsu mai dafi kamar kibiya,
don su yi wa mara laifi kwanton ɓauna, * su hallaka shi kwatsam, ba tsoron Allah.
Suna shirya masa magani mai dafi, * suna kakkafa masa tarkuna,
suna cewa: “Wanene ke ganinmu? * Wa zai binciki daidaitaccen sharrinmu?”
Amma Mai Bincike zai binciki * can cikin cikin mutun * har cikin birnin zuciya.
Ɗaukaka ga Allah Mai Kibau! * Ka ninka raunukansu!
Maɗaukaki zai sa matsegunta su yi tuntuɓe, * dukan masu girman kai za su ƙasƙanta.
Kowane mutun zai ji tsoro, * ya bayyana aikin Allah, * ya riƙa tunanin aikinsa.
Bari mai adalci ya yi murna da Yahweh, * ya nemi tsira a gunsa! * Bari dukan masu zuciyar kirki su more!
Zabura ta 65
Yabo gare ka a mafakarka ta samaniya, * da can Sihiyona, ya Allah.
A gun ka za a cika wa’adodi, * domin ka kan ji addu’o’i.
A gare ka duk bil’adama * zai kai miyagun ayyukansa.
Ayyukanmu na tawaye sun yi yawa, * ka gafarta mana!
Mai albarka ne wanda ka zaɓa zuwa kusa da kai, * don ya zauna a majalisarka.
Bari mu gamsu da kyan gidanka, * da tsarkin Haikalinka.
Lokacin shari’a ka nuna mana al’ajibanka, * ya Allahnmu mai nasara!
Kā shimfiɗa dukan kusurwoyin duniya, * da na nesan teku.
Kā kakkafa duwatsu da ikonka, * sun yi ɗamara da ƙarfinka.
Kā kwantada da haukan teku, * da haukan raƙuman ruwansa, * da kuma tarzomar mutane.
Mazaunan bangon duniya sun ji tsoro * saboda al’ajibanka.
Ka sa gamzaki da tauraron dare * su yi sowar murna.
Ka ziyarci ƙasa, * ka sa ta tsalle don murna, * ka sa ta yi albarku da ruwan samanka.
Ka cika magudadar sama da ruwa, * ka wadaci ƙasa da hatsi, * gama kā kafa ta don wannan.
Ka malalo ruwa a kwarin gona, * ka jiƙa kunyoyinta.
Ka tausasa ta da ruwa mai yawa, * ka albarkaci hatsinta!
Ka albarkaci tuddai da ruwan samanka, * makiyayunka sun ba da mai.
Dajin Allah ya tsatso da mai, * ka lulluɓi tuddai da murna.
Ka sa kwaruruwa su cika da dabbobi * ƙasar kwari kuwa alkama.
Bari su ta da murya, * su yi sowar farinciki.
Zabura ta 66
Yi sowar farinciki ga Allah, ke duniya duka, * yi waƙar ɗaukaka sunansa, * yi shelar ɗaukaka yabonsa.
A ce, “Ya Allah, * mai ban tsoro ne kai ta ayyukanka!
Saboda girman ikonka, * magabtanka suna sunkuyawa don tsoro a gabanka.
Dukan duniya tana bauta maka, * tana yi maka waƙa, waƙar sunanka.
Ku zo, ku ga ayyukan Allah, * mai firgita ’yan’adan ta ayyukansa.
Ya mai da teku busasshiyar ƙasa, * suka taka ƙasar kogin suka haye. * Ku zo, mu yi farinciki a cikinsa!
Yana sarauta daga madauwamiyar mafakarsa, * idanunsa na kallon al’ummai, * don kada ’yan tawaye su tayar masa.
Ku yabi Allahnmu, ya ku mutane, * da murya mai ƙarfi ku yabe shi!
Wanda ya lissafa mu a cikin rayayyu, * bai ma sa ƙafafuna cikin Lema ba.
Amma kā gwada mu, ya Allah, * kā jarraba mu kamar yadda ake tace azurfa.
Kā kai mu cikin hamada, * kā sa marurai a gindinmu.
Kā sa ciwo ya hau kanmu, * mun ratsa wuta da ruwa, * bayan ka fishe mu daga wurin wadata.
Zan shiga gidanka da ƙonannun hadayuna, * in cika wa’adodina,
waɗanda na faɗa da leɓunana, * bakina ya furta a lokacin wahala.
Zan miƙa maka dabbobi masu kiɓa don a ƙona, * da ƙamshin raguna da aka ƙona. * Zan shirya bajimai duk da awaki.
Ku zo, ku ji, dukanku masu tsoron Allah, * zan gaya maku abin da ya yi mani.
Da bakina na yi kuka gare shi, * muryaoyin waƙa kuma suna kan halshena.
Da na tabbata mugunta a zuciyata, * da Ubangiji bai ji ni ba.
Amma Allah ya ji ni, * ya saurari muryar addu’ata.
Albarka ga Allah! * domin bai ƙi addu’ata ba, * zan sake faɗin alherinsa har sau ɗari.
Zabura ta 67
Allah ya ji tausayinmu, ya yi mana albarka, * ya zo mana da hasken fuskarsa.
In an san sarautarka a duniya, * da nasararka a cikin dukan al’ummai,
mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.
Al’ummai za su yi farinciki da sowar murna, * domin kai ne sarki.
Za ka kai al’ummai Sararin, * jama’a kuma cikin Ƙasar.
Mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.
Bari ƙasa ta ba da amfaninta, * Allah, Allahnmu, ya yi mana albarka.
Allah ya yi mana albarka, * dukan ƙasashe su ji tsoronsa * har bangon duniya.
Zabura ta 68
In Allah ya tashi, * magabtansa sukan watsu, * maƙiyansa sukan guje shi.
Kamar yadda hayaƙi ke bin iska, su ɓace, * kamar yadda danƙo ke narkewa a gaban wuta.
A gaban Allah * miyagu sukan san inda dare ya yi masu.
Amma masu gaskiya za su yi murna, * su sami tagomashi a gaban Allah, * za su yi waƙa mai farinciki.
Ku yi waƙa, ku alloli, * ku raira yabo, ku sammansa, * ku share hanya ga Mai Hawan Giza-gizai.
Ku ji yi murna da Yahweh, * ku yi murna a gabansa!
Allah daga tsattsarkan mazauninsa * shi ne uban marayu da mai kare gwauraye.
Allah wanda ya ba mai kaɗaici gida, * shi ya ’yanto ’yan sarƙa tare da waƙa
Amma masu taurin kai, * an binne su a Hamada.
Ya Allah, sa’ad da ka fita * gaban mutanenka, * da ka ƙetare hamada,
sai ƙasa ta raunana, * sammai kuma suka saukad da ruwa
da ganin Allah, * Mai Sinina,
da ganin Allah, * Allah na Isra’ila.
Ya Allah, ka aiko da ruwan samanka mai yawa, * ƙasarka da sarautarka, ka tabbatad da su.
Ka wadaci jama’arka da ke zaune a kai, * da ruwan samanka ka arzuta mazaunanta, ya Allah.
Allah ya aike da magana, * mai faranta rundunar taurari.
Sarakunan rundunarsu su sauko da ruwa, * wurin kiwon kasar ya sami rabonsa na albarka.
Bari su zube * a tsakar garken tumaki
An dalaye fukafukan kuruciya da azurfa, * da gashinta kuma da zinariya.
Sa’ad da Shaddai ya inuwantad da sarakuna, * dusar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmona.
Ya babban dutse, Dutsen Bashan, * ya dutse mai yawan tulluwa, Dutsen Bashan,
don me kake kallo da hassada, * ya dutse mai yawan tulluwa,
dutsen da Allah ya zaɓa don mazauninsa, * inda Yahweh zai zauna har abada.
Karusan Allah dubu ishirin ne, * maharban Ubangiji dubbai ne, * wanda ya kafa Sinina mabautarsa.
Kā hau sama, * kā jawo kamammu.
Kā karɓi kyautai daga hannuwansu, * amma Yahweh Allah ya binne masu taurin kai.
Albarka ga Ubangiji yau da kullun, * Allah kansa, Macecinmu, ya cire mana nauyin kayanmu.
Allah kansa shi ne Allah na cetona, * tun da Ubangiji Yahweh ya sa mu tsira daga mutuwa.
I, Allah ya buge kan magabtansa, * ya farfashe kwakwalunsu, * sa’ad da ya fito daga sammansa.
Allah ya ce, “Na taushe Macijin, * na kwantad da Teku Mai zurfi.”
Haka, ƙafarka ta ragargaji gaɓoɓinsu, * harsunan karnukanka kuma sun sami rabo gun magabtanka.
Ku ga faratin Allah, * faratin Allahna, * Sarkina daga mabautarsa.
Mawaƙa suna kan gaba, * mabusa a baya, * a tsakiya ’yan mata suna kiɗa.
A taruwar jama’a ku yabi Allah, * Yahweh kuwa a taron Isra’ila.
Ga Biliyaminu ƙarami, yana yi masu jagora, * sarakunan Yahuda kuma a jeri biyu,
sarakunan Zabaluna, * da sarakunan Naftali.
Ya Allah, ka aiko mana da ƙarfinka, * ƙarfi, ya Allah, abin da ka gina domin mu.
Haikalinka, ya Maɗaukaki, a Ƙudus yake, * sarakuna za su kawo maka kyautai.
Ka tsawata wa dabbar lema, * taron bajimai da maruƙansu.
waɗanda ke tattaka mutane saboda sha’awar azurfa, * suna warwatsa mutane don marmarin yaƙi,
Bari attajiran Masar su kawo shuɗin zane, * Habasha ta rugo ta kawo kayanta ga Allah.
Ku sarakunan duniya, ku yi waƙa, * ku alloli, ku raira yabbai ga Ubangiji.
Ku dubi Mai Hawa sammansa, * sammai na tun fil’azal.
Ku saurara, yana aiko muryarsa, * murya mai girma!
Ku girmama Allah, * Maɗaukakin Isra’ila.
Ɗaukakarsa da ikonsa * sun fi ƙarfin sama. * Allah mai bantsoro ne a tsattsarkan mabautarsa.
Hakika shi Allah ne na Isra’ila, * wanda ke ba da nasara da iko. * Ku mutane, ku yabi Allah!
Zabura ta 69
Ka cece ni, Allah, * domin ruwa ya kai wuyana.
Na nutse cikin Taɓo mai zurfi, * inda ba damar tsayawa.
Na shiga zuzzurfan ruwa, * inda igiyoyin ruwa suke cina.
Na gaji da kuka, * maƙogwarona ya bushe.
Idanuna sun fara dushewa, * sa’ad da nike dako, ya Allah.
Magabtana masu makirci sun yi yawa, * fiye da gashin kaina.
Fiye da gashin kaina * mayaudarana suka zarce da yawa.
Abin da ban sata ba, * dole ne in mayas da shi?
Ya Allah, ka san barancina, * laifofina ma ba a ɓoye suke gare ka ba.
Kada masu sa zuciya gare ka su sha kunya * saboda ni, ya Ubangiji Yahweh Mai Runduna.
Kada masu nemanka su kunyata * saboda ni, ya Allah na Isra’ila.
Saboda kai ne na sha zagi, * cin mutunci ya rufe fuskata.
Na zama baƙo ga ’yan’uwana, * bare kuma ga ’ya’yan da muke uwa ɗaya.
Gama kishi domin gidanka ya cinye ni, * zage-zagen masu zaginka sun taru a kaina.
Ina tunanin dukan ɓacin raina a cikin azumina, * wulakanci kuma ya zama rabona.
Na mai da tsummoki tufafina, * na zame masu abin dariya.
Har ’yan bikin da mashaya * suna wallafa waƙoƙin shegantaka a kaina.
Amma ni kam, addu’ata gare ka take, Yahweh, * ya Allah, ka nuna mani alherinka yanzu.
Da ƙaunarka mai girma * ka amsa mani * da amintaccen taimakonka.
Ka cece ni daga Caɓin, * kada in nutse.
Bari a kuɓutad da ni daga Maƙiyi, * daga zurfafan ruwaye ma.
Kada juyewar ruwan teku ta rufe ni, * ko zurfinsa ya haɗiye ni, * ko Ramin ya rufe bakinsa a kaina.
Ka amsa mani, Yahweh, * domin ƙaunarka mai girma ce.
Bisa ga yawan rahamarka, * ka juyo fuskarka gare ni.
Kada ka juya * wa bawanka baya.
Ka amsa mani da sauri, * don wahalar da ke damuna,
Ka kusato ni, ya Allah, ka cece ni, * ka fanshe ni daga Mazaunin Magabcina.
Ka san wulakancin da ake yi mani, * kunyata da ƙasƙancina a gabanka suke.
Wulakanci ya lalata kayan cikina, * ciwo ya dagargaji zuciyata.
Na nemi mai jin tausayi, amma babu, * da mai sanyaya zuciya, amma ban sami wani ba.
Sun sa dafi a abincina, * don ƙishinruwana sun miƙa mani ruwan tsami.
Bari teburin abincin da ke gabansu ya zama tarko gare su, * abokan tarayyarsu kuma su zaman masu taru.
Idanunsu su dushe don kada su gani, * cinyansu kuma su yi ta rawa kullun.
Ka jibga masu haushinka, * bari tsananin hushinka ya cim masu.
A sansaninsu kada wani ya ragu, * a tantunansu kada wani ya zauna.
Domin wanda ka buge sun tsananta masa, * azabar wanda ka raunata kuwa suna ta tsegumi a kai.
Ka hukunta su da sharri bisa sharri, * kada su shiga aljannarka.
Bari a share sunayensu daga littafin rai, * kada a sa a cikin adalai.
Amma ni gajiyayye ne, cikin azaba, * taimakon Allah ya tallafe ni,
don in yabi sunan Allah da waƙa, * in ɗaukaka shi da godiya.
Wannan zai daɗaɗa ran Yahweh fiye da takarkari, * ko fiye da bajimin sa mai ƙahoni da kofatai.
Ku duba, ku gajiyayyu, * bari masu neman Allah su yi farinciki, * zukatansu su tofu!
Domin Allah yana sauraren mabukata, * Yahweh baya ya da waɗanda ke nasa.
Bari sama da ƙasa su yabe shi, * tekuna da dukan abin da ke motsi a cikinsu.
Hakika, Allah zai ceci Sihiyona, * zai sake ginin garuruwan Yahuda, * waɗanda aka kora za su koma su zauna ciki.
Jikokin bayinsa za su gaji birnin, * za su zauna ciki, su mallake shi.
Zabura ta 70
Ya Allah, ka cece ni, * Yahweh, ka yi hanzari ka taimake ni!
Bari masu neman raina * su kunyata, su ruɗe.
Bari masu sha’awar lalacewata * ƙasƙanci ya zama nasu.
Ƙaiƙai ya koma wa masu tseguman banza, * waɗanda ke ce mani, “Ga shegen nan, ga shegen nan!”
Bari dukan masu nemanka * su yi farinciki, su yi murna da kai!
Bari dukan masu son cetonka * su riƙa cewa: “Allahu akbar!”
Amma ni, da ke gajiyayye da mabukaci, * ya Allah, ka hanzarto zuwa gare ni.
Kai ne mataimakina da macecina, * Yahweh, kada ka yi jinkiri.
Zabura ta 71
Yahweh, a gare ka nike dogara, * kada in kunyata, ya Madauwami!
Da amincinka ka kuɓutad da ni, ka fanshe ni, * ka kasa kunne gare ni, ka cece ni.
Dutsen Taimako, ka zama nawa! * Kā alkawalta zuwa guna a kowane lokaci.
Ka cece ni yanzu! * gama kai ne dutsena da mafakata.
Ya Allah, ka ’yanta ni daga hannun mugu, * daga kagen azzalumi da ɗan fashi.
Gama kai ne begena, ya Ubangiji, * Yahweh, madogarata ne tun a cikin kuruciyata.
Kai ne ka tallafa mani tun daga mahaifa, * daga cikin uwata kai ka lura da ni, * zan dinga yabonka.
Na zama zakaran gwajin dafi ga maharɓa, * amma kai ne ƙaƙƙarfar mafakata.
Bakina ya cika da yabonka, * da na al’ajibanka yini zubut.
Kada ka watsad da ni da tsufana, * in ƙarfina ya gaza, kada ka yashe ni.
Magabtana suna hararata, * masu neman raina suna ƙulla shawara da juna,
suna cewa: “Allah ya yashe shi, * mu fafare shi, mu kama shi, * domin babu mai ceto.”
Ya Allahna, kada ka yi nesa da ni, * ya Allahna, ka hanzarta taimakona.
Bari matseguntana * su sha kunya tuli.
Masu neman lalacewata * su kwashi muzanci da kunya.
Amma ni a kullun zan sa zuciya gare ka, * in dinga yabonka ba fashi.
Bakina zai lissafta ayyukanka masu aminci, * wuni zubut kuma dukan aikinka na ceto, * duk da ba zan iya lissafa su ba.
Zan shiga babban gidanka, ya Ubangiji, * Yahweh, amincinka kaɗai zan yi shela.
Ya Allah, kā hore ni tun daga ƙuruciyata, * har yanzu ma ina ba da labarin al’ajibanka.
Har cikin tsufana da furfura, * kada ka yashe ni, ya Allah,
sai na ba jama’a labarin ikonka, * ga duk wanda zai shiga ƙaton gidanka.
Ya Allah, amincinka ya kai har sama, * domin ka aikata manyan abubuwa. * ya Allah, wa ke kama da kai?
Ko da yake ka nuna mani * wahalu masu yawa da husumai da cuta,
za ka sake raya ni, * daga zurfafan Ƙalƙashin Ƙasa kuma * za ka sake ta da ni.
Ka ji daɗin babban baikona na shanu, * ka ma lulluɓe ni da tausayinka.
Da babbar murya zan yabe ka da garaya, * in yabi amincinka, ya Allah.
Zan yabe ka da molo, * ya Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Leɓunana za su yi waƙa, * i, zan yabe ka, * duk da ruhuna da ka fanso.
Da babbar murya halshena zai lissafta * ayyukanka masu aminci yini zubut.
Ka sa su sha kunya, * duk masu marmarin lalacewata, * ka sa su ruɗe.
Zabura ta 72
Ya Allah, ka ba sarki hikimar yanke hukuncinka, * ɗan sarki kuma ya san gaskiya,
don ya hukunta mutanenka da gaskiya, * zaluntattu kuma da adalci.
Bari duwasu su kawo wa mutanenka salama, * tuddai kuma adalci.
Bari ya kare waɗanda aka zalunta * ya ceci ’ya’yan mabukata, * ya dami azzalumi.
Ka sa ya girmama ka muddin daɗewar rana, * har wanzuwar wata, * zuwa zamanin zamanu.
Bari ya sauko kamar ruwan sama a kan ciyawa, * tamkar yayyafi a kan busasshiyar ƙasa.
Bari adali ya bunƙasa a zamaninsa, * salama kuma ta kasance muddun wata na wanzuwa.
Bari ya yi mulki daga teku zuwa teku, * daga Kogin Yufiretis har zuwa ƙarshen duniya.
Bari kabilun hamada su durƙusa masa, * har sai magabtansa sun ci turɓaya.
Sarakunan Tarshishi da na tsibirai * su kakkawo masa haraji.
Sarakunan Shiba da na Saba * su ba shi kyautayi.
Dukan sarakuna su durƙusa a gabansa, * dukan al’ummai su bauta masa!
In ya ceci mabukacin da ke kuka, * da zaluntaccen da ba shi da mataimaki,
in ya ji tausayin matalauci mabukaci, * har ya ceci rayukan yasassu,
in ya ceci rayukansu daga zalunci, * jininsu kuwa yana da daraja a gare shi,
daga nan ransa ya daɗe! * ya sami kyautar zinariya daga Shiba,
a dinga yi masa add’ua ba fāshi, * ana roƙa masa albarku kullun.
Bari mayafin alkama ya rufe ƙasar, * da haki mai yawa a kan tuddai.
’Ya’yansa su yi fure kamar icen Labanan, * suna yin toho kamar ciyawa.
Bari jikokinsa su ɗade har abada, * suna haifuwar ’ya’ya har ran da rana ta ƙare.
Bari jikokinsa su sami albarka saboda shi, * dukan al’ummai su yi murna ta wurinsa.
Albarka ga Allah Yahweh! * Allah na Isra’ila, * mai aikata al’ajibai shi kaɗai.
Albarka ga sunansa mai ɗaukaka har abada! * Bari duniya duka ta cika da ɗaukakarsa.
Zabura ta 73
Ya Isra’ila, lalle Allah yana kyautata * wa masu tsattsarkar zuciya.
Amma sawayena sun kusa yin tuntuɓe, * ƙafafuna sun kusa gocewa,
sa’ad da na ji ƙyashin masu fankama, * har na ga ƙwanjin dukiyar miyagu.
Ba su da faɗi-tashi, * jikinsu yana da ƙarfi da sulɓi.
Ba su yin aikin bayi, * ba a tsananta masu kamar sauran ’yan’adan.
Don haka alfarma ta zamam masu sarƙar wuya, * tufafin zalunci ya rufe su.